• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Bawa Kungiyoyin Sa Kai Dama Ne Zai Kawo Karshen Masu Kwacen Waya a Kano — Kwamadan Kungiyar Mafarauta

ByGlobal Tracker

May 30, 2023

Kungiyar tsaro ta Mafarauta ta kasa ta ce bawa Kungiyoyin Sa Kai Dama a tabbatar da tsaron unguwanni da yankuna na kwaryar birnin Kano da Kewaye ne zai kawo karshen matsalar Kwacen Waya da yake damun alumma a wannan lokaci.

Kwamadan Kungiyar Mai kula da yankin Arewa maso yammacin Nigeria Abdullahi Al-Ameen ne ya bayyana hakan a zantawarsa da GLOBAL TRACKER.

A cewar Abdullahi, bawa kungiyoyin sa kai da kungiyoyin uguwanni dama da kuma samar musu da kayan aiki zai taimaka matuka wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin alumma.

“Bawa kungiyoyi na unguwanni, kwamitocin tsaro na yankuna dama zai tallafawa, kowacce unguwa matukar ta tumbatsa zaka ga tana da irin wadannan kungiyoyi, kamar VIJALANTEE wanda dama sun Dade, akwai KUNGIYAR TSARO TA MAFARAUTA (NIGERIAN HUNTERS AND FOREST SECURITY SERVICE, NHFSS), kamar KUNGIYAR MU HADU MU GYARA, kai akwai unguwanni ma da manyan mutane ne da kansu da daddare suke fitowa su kare yankunan su, kaga ire-iren wadannan ya kamata a tallafawa su day kansu zasu kare yankunan su,” inji Abdullahi Al-ameen.

KU KARANTA: Bawa NHFSS Damar Samar Da Tsaro a Lokacin Zabe Zai Kara Mana Karfin Gwiwa — Abdullahi Al-ameen

Ya ce “wadannan kungiyoyin tallafin da su ke nema kayan aiki ne, wasu abin hawa suke nema saboda idan sun kama Mai lefin su kaiwa yan sanda Shi, wasu kuma makamai suke nema, domin zaka ga wani Bata garin da wani makamin da baka taba ganin irin sa ba, kaga kenan Dole sai ka shirya, wasu kuma babbar matsalar su shine da sun kama sun kaiwa jami’an tsaro sai suga an sako su, to wannan ne yake damun alumma a harkokin tsaro.”

Kwamandan ya bukaci hukumomin tsaro da su saka tsoron Allah a ransu tare da yin aiki bisa gaskiya da amana, yana Mai cewar “tsaron nan a yi shi bisa gaskiya da rikon amana, kuma ba sani ba sabo, babu batun danka ko dan uwanka ko yayan ka ko kuma kanin ka, duk wanda yayi lefi ayi masa hukuncin dai-dai abun da ya aikata, to ta haka ne za’a samu karancin aikata lefuka musamman a jihar Kano.”

Abdullahi Al-ameen ya cigaba da jan hankali mahukunta da su dauki mataki Mai tsauri akan masu satar waya ko kwacen ta domin aikata lefin ne babba la’akarin da yadda kwacen wayar yayi sanadiyyar mutuwar mutane masu amfani a tsakanin alumma.

“Ku san ince wallahi duk inda ake kwacen wayar nan an sani, an san inda ba’a fito da waya, an san inda da yuwa kaje da waya ka dawo lafiya, an san inda ake fito da waya kayi komai da ita ba tare da matsala ba, saboda haka ya kamata a saka kwararrun Ma’aikata a yankunan ake aikata kwacen wayar nan, idan ma jami’an tsaro za’a saka su rika sintiri da kai-kawo da yaki da matsalar nan to yakamata ayi domin idan abun nan ya ci gaba zata kai ga lokacin da babu wanda zai iya fitowa da waya kuma yaran nan sun sani ya kuma koma da ita lafiya, zata kai ga lokacin da yawo mai sai ya gagari mutane,” inji Kwamandan.

KU KARANTA: KANO: Mun Shirya Tsaf Don Nishadartar da Masu Bude Ido — Shugaban Hukumar Kula da Gandun Daji

Kwamandan yayi fatan manyan Kano da dattawan garin, da manyan kungiyoyi kamar su “Arewa Consultative Forum” da su “Kano Lead” da sauran masu ruwa da tsaki zasu bada gudun mowa domin shawo kan matsalar kwacen waya da yanzu ya addabi al’ummar jihar Kano.

Abdullahi Al-ameen dai shike kwamandan kungiyoyi a jihohi 7 na Arewa masu yamma da suka hadar da Kano da Jigawa da Kaduna da Katsina da Sokoto da Kebbi da Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *