• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Mulkin Abba K. Yusuf na Sa’o’i 24 Ya Nuna Kishin Sa Da Cigaban Kano — Shafi’u Kura

ByGlobal Tracker

May 31, 2023

DAGA: YAHAYA SADISU ALKASIM, KANO.

 

Dan takarar Shugaban karamar hukumar Ungogo Honarabil Shafi’u Hussaini Kura ya taya gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf Murnar rantsar da shi da akayi tare da Yi masa addu’o’in gudanar da mulki cikin Nasara.

Shafi’u Kura ya bayyana hakan ne a lokacin da ya hada liyafar cikin abinci domin taya murna ga sabon gwamnan Kanon, yana mai cewa salon mulkin Abba na Sa’o’i 24 ya nuna cewa shi mai kishin jihar Kano ne da al’ummar ta.

A cewarsa, la’akari da irin yadda aka tara mutane masu dimbin yawa da a sama da shekaru 8 ba’a samu irin sa ba domin gwamnati ce da mutane suka zaba kuma suke shaukin zuwan ta da nufin gudanar da ayyukan raya kasa.

“A cikin Sa’o’i 24 abba, ya ziyarci Ma’aikatu daban-daban, ya dawo da kunna wasu fitulun hanya da suka shafe shekaru 4 ba’a kunna su, ya ziyarci cibiyar gyaran Hali da tarbiyya ta Kiru, ya ziyarci makabartu, da sauran gurare,” inji Shafi’u Kura.

KU KARANTA: Yan Kasuwa a Ungogo Sun Ta Ya Abba K. Yusuf Murnar Lashe Zabe

Dan takarar ya kuma ba tabbacin cewa matukar ya sami nasarar zama Shugaban karamar hukumar ta Ungogo akwai tsare-tsare da dama za ya shirya gudanarwa na bunkasa tattalin arzikin yankin da samarwa da matasa aikin yi.

“Zamu samar da hanyoyin bunkasa kananan sana’o’i da cigaban matasa, da yaki da matsalar tsaro da kwacen waya da tallafawa masu karamin karfi da tallafawa mata masu juna biyu a asibitocin mu,” inji Kura.

Daga nan ya bukaci hadin kan masu riwa da tsaki na jam’iyar NNPP Mai alamar kayan marmari da jagororin jam’iyar a al’ummar karamar hukumar ta Ungogo domin samun Nasara inda yayi alkawarin karbar shawarwari daga wajen su don gudanar da ayyukan cigaban yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *