DAGA: IBRAHIM ABUBAKAR DISO
Shugaban Hukumar Jindadin Alhazai ta jihar Kano Alhaji Laminu Rabi’u Dan-Baffa ya bayyana takaicin yadda tsohon Shugaban Hukumar ya Siyarwa Maniyata kujeru fiye da wadanda aka Warewa jihar Kano.
Laminu Dan-Baffa ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da wakilin GLOBAL TRACKER a Kano.
Ya ce an warewa jihar Kano kujeru 6,082 amma tsohon Shugaban hukumar ya sayar da kujeru 6,273 wato an sami karin kuje 191.
“An bawa Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano kujeru 6,082 amma bisa ganganci tsohon sakataren hukumar ya sayar da kujeru 6,273, wato an sami karin dari da casain da daya (191), wanda hakan tasa dole abar wasu maniyyatan a kasa.
KU KARANTA: Za’a Kara Kudi Idan Yakin Sudan Ya Kai Lokacin Hajji – NAHCON
Tunda fari, tsohon sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano Alhaji Abba Danbatta ya godewa Allah akan damar daya samu na Jan ragamar Hukumar na tsawon shekaru, ya kara da cewa “shi mulki tamkar numfashi ne wani yana fita wani yana shiga a don haka Allah ya kawo karshen zaman sa a wannan Hukumar kuma ina roki ma’aikatan Hukumar dasu bawa sabon babban daraktan hukumar hadin kai.
Danbatta ya yiwa sabon daraktan hukumar fatan alheri.
A nasa jawabin, shugaban hukumar gudanarwa na hukumar Alhaji Yusuf Lawan ya godewa tsohon sakataren hukumar bisa hadin kai daya basu a yayin jan ragamar Hukumar, inda ya kara da cewa rahotanni daya mika musu zasu bincika idan akwai inda basu gane ba zasu tantube shi domin neman karin bayani.