• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Janye Tallafin Man Fetir: Ku Kwantar Da hankalin Ku Abubuwa Za Su Daidaita — Mamuda Zangon Kabo

ByGlobal Tracker

Jun 11, 2023

Kungiyar masu sana’ar magunguna ta jihar Kano dake malam kato ta yi kira ga alummar Najeriya, da su kwantar da hankulansu sakamakon tashin gwauran zabi da man fetur yayi saboda cire tallafin mai da Gwamnatin tarayya tayi.

Shugaban Matasa na Kungiyar Alhaji Mamuda Zangon Kabo ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da wakilin GLOBAL TRACKER.

Zangon Kabo ya ce kamata yayi alummar Najeriya su ci gaba da gudanar da addu’oin samun sauki daga wajen Allah subahanahu wata’ala kasancewar ita ce kawai mafita ga yan Nigeriya.

KU KARANTA: Buhari Ya Kaddamar Da Aikin Hakar Man Fetir a Nassarawa

Shugaban ya bayyana cewa akwai bukatar a duba lamarin da alummar Najeriya suka sami kansu a ciki ne saboda halin matsin rayuwa domin wasu daga cikin alumma sai sun fita za su samu abin da za su ciyar da iyalansu wadanda akasari sune suka fi yawa.

Mamuda ya ce akwai kananan yan kasuwa da suke da karancin jari da za su gudanar da sana’oin su na yau da kullum a samar da hanyoyin da za’a tallafa musu.

Haka zalika ya shawarci masu kananan sana’oi da yan kasuwa da su kasance masu yin lissafi a kasuwancin su na yau da kullum domin fahintar yadda yake tafiya, Wanda yin hakan zai taimaka musu wajen sanin inda suka dosa.

Daga nan ya shawarci kungiyoyin yan kasuwa da manyan yan kasuwa da su kasance masu tallafawa kananan yan kasuwa na kasa da suke da karancin jari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *