• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Kakani Na Suna Dori Sama Da Shekaru 250 — Sarkin Dorin Kano

ByGlobal Tracker

Jun 11, 2023

Sarkin Dorin Kano Alhaji Uba Muhammad Kofar Na’isa ya ce Kakanin sa suna Sana’ar Da sarautar Dori sama da shekaru 250 da suka gabata kuma sunyi Nasara sakamakon yadda suke saukakawa alumma.

Uba Muhammad ya bayyana hakan ne lokacin da Shugabanin Kungiyar masu maganin gargajiya ta kasa reshan Karamar hukumar Gwale (NANTMP) suka kai masa ziyara a fadarsa.

Sarkin ya bukaci Madora Da Masu Maganin Gargajiya Su Rinka Zurfafa Bincike Domin Ingantuwar Sana’ar su day kuma kula da lafiyar al’ummar da suke yiwa aiki.

Ya ce ta hanyar kiyayewa da ka’idojin aikin da neman Karin ilimi gami da sanya tausayi ga al’umma kawai shine zai bukasa tare da dorewar sana’ar.

Kofar Na’isa yayi magana mai tsaho dangane da tarihin sana’ar dori da kuma yadda ta ke bunkasa har ya zuwa wannan zamani. Haka kuma ya yi alkawarin bada duk taimakon da ya kamata ga Kungiyar.

KU KARANTA: Janye Tallafin Man Fetir: Ku Kwantar Da hankalin Ku Abubuwa Za Su Daidaita — Mamuda Zangon Kabo

“Sana’ar Dori ta samo asali tun zamanin Manzon Allah Annabi Muhammad (S.A.W), kuma harkar Dori an dade ana Yi a gidan nan domin sama da shekaru 250 kakanina da Kakanin su suke yin dori,” inji Sarkin Dorin Kano.

Ya Kuma godewa masarautar Kano, karkashin jagoranci Alhaji Aminu Ado Bayero, bisa tallafi da goyan baya da take bawa masu sana’ar gargajiya a jihar nan.

Da yake jawabi Shugaban Kungiyar masu maganin gargajiya ta kasa reshen Karamar hukumar Gwale, Dakta Adamu Yusuf Kakan, ya ce sun gabatar da kansu ga fadar Sarkin Dori domin su jaddada mubaya gare shi tare da karin samun hadin Kai don tallafawa al’ummar jihar Kano da ma makwanta baki daya.

Ya godewa Sarki tare da alkawarin samar da cibiyar da zata hada kan masu sana’ar gargajiya a Karamar hukumar ta Gwale domin ci gaba da taimakon jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *