• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Da Dumi-Dumi: Kwankwaso da Abba Sun Goyi bayan Falgore Ya Zama Shugaban Majalisar Dokokin Kano

ByGlobal Tracker

Jun 12, 2023

Jagoran jam’iyar NNPP kuma dan takarar Shugaban kasa a zaben da ya gabata Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf da ma dukkan yan takarar shugabancin Majalisar Dokokin jihar sun amince tare da goyon bayan J.S Fargore domin zama sabon Shugaban majalisar.

Rahotanni sun ce amincewar ta biyo bayan tattaunawar da dukkan masu ruwa da tsaki a jam’iyar NNPP suka Yi a daren nan.

Haka kuma mataimaki na musamman ga Dan majalisar tarayya Mai wakiltar Rano da Kibiya da Bunkure a majalisar wakilai ta kasa Fatihu Yusuf ya tabbatarwa da GLOBAL TRACKER tattaunawar.

Falgore dai shine Dan majalisa da zai wakilci karamar Hukumar Rogo a majalisar wanda za’a rantsar da su a talatar nan.

Akwai Karin bayani…..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *