DAGA: IBRAHIM SANI GAMA, KANO
Kungiyar Marubuta labarin Wasanni ta kasa reshen jihar Kano ta shirya gasar Wasanni tsakanin kungiyoyi daban-daban a jihar da nufin tabbatar da zaman lafiya tsakanin manya da kananan Kabilun dake Kano.
Sakataren kungiyar Abdulgafar Oladimeji ne ya bayyana hakan bayan mika kayan wasanni ga wasu daga cikin kungiyoyin da suke cikin gasar wanda ya gudana a nan Kano.
Abdulgaffar Oladimeji ya bayyana cewa, Sarkin Yarbawa na jihar Kano da kamfanin (BETWGB) suka dauki Nauyin gasar
Wanda aka yiwa Lakabi da samar da zaman Lafiya.
Ya ce an samar da gasar ne domin sada zumunta da zaman lafiya tsakanin alumomi da kabilu daban daban dake Nigeria, musamman na jihar.
Ya bayyana cewa, wannan sabuwar gwamnati mai ci sai tayi aiki tukuru wajen bijiro da tsare-tsare da za su taimaka wajen bunkasar harkokin wasanni na jihar, musamman kwallon kafa Wanda matasa ne suke yinta koda yaushe inda ya ce, Sarkin Yarbawa da kamfanin sune suka dauki nauyin kyaututtukan da aka rabawa kungiyoyin kwallon kafar sakamakon jajircewa da kwazo da suke nunawa wasannin.
KU KARANTA: LABARI-DA-HOTUNA: Yadda Aka Nada Ibrahim Yaro D/tofa Talban Alajawa a Bagwai
Ya kara da cewa daga cikin kyautukan da aka rabawa kungiyoyin, akwai riguna da kalanda da sauran kayayyakin da suka shafi kwallon kafa, Inda ya bayyana cewa, kungiyoyi da dama sun samu kyaututtukan kamar kananan hukumomin Kibiya da Takai da Sumaila da Gwale da kuma wasu kungiyoyin kwallon kafa na wasu daga cikin jihohin Najeriya, kamar jihar Kwara da dai sauransu.
A jawabinsa, Sarkin Yarbawa Dakat Murtala Alimi Otutesi ya sha alwashin ci gaba da ba da tallafawa kungiyoyin kwallon kafar domin samar da hadin kai da zaman lafiya tsakanin alumma.
Dakta Murtala ya kuma bayyana cewa, za su kara tattaunawa da Ibrahim Galadima a matsayinsa na Uba kuma, Masani a harkokin wasanni yadda za su hada hannu guda domin baiwa Shugabannin kungiyoyin kwallon kafa horo na musamman domin yin gogayya da sauran kungiyoyin wasan kwallon kafa na kasashen Duniya.
Ya ce rashin baiwa Shugabannin kungiyoyin kwallon kafa horo na daya daga cikin abubuwan da suke mayar da Nigeria kuma baya a fannin harkokin wasanni.
Haka zalika, Sarkin Yarbawan ya yabawa kungiyar marubuta wasanni da kwamatin shirya gasar, Musamman Abdulgaffar Oladimeji daya taimaka wajen ganin komai ya tafi yadda ya kamata inda ya ce ya dade yana ba da gudunmawa a harkokin wasanni yadda ya dace.