• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Zamu Yaki Dukkan Matsalolin Da Ke Damun Makarantun Addini a Yankin Mu — Sarkin Bichi

ByGlobal Tracker

Jun 15, 2023

DAGA: ZAHARADEEN SALEH, KANO

 

Mai martaba Sarkin Bichi a jihar Kano dake arewacin Nigeria Alhaji Nasiru Ado Bayero ya ce masarautar Bichi zata dauki dukkan matakan da suka da ce domin yakar Matsalolin da ke damun Makarantun Addini a yankin da nufin cigaban addinin Musulunci.

Nasiru Ado Bayero ya bayyana hakan ne lokacin saukar karatun Al-Qur’ani Mai girma na dalibai saba’in da bakwai (77) a makarantar islamiyya ta Ta’Awunul Umman litihafizul Qur’an dake unguwar kanawa kofar Arewa Bichi.

Cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun Masarautar Rulwanu Idris Malikawa Garu ya aikowa wakilin GLOBAL TRACKER ta ambato Mai martaba Sarkin na cewa akwai bukatar iyayen Yara dake makarantar su rinka taimaka wa makarantar da kayan aiki.

Mai Martaba Sarkin ya bayyana muhimmancin karatun Al-Qur’ani da Kuma koyar dashi, inda ya bukaci daliban da sukayi saukar da su cigaba da Neman illimi.

Ya Kuma bayyana jindadi dangane da baiwar da Allah Ya yiwa Bichi da makarantun Al-Qur’ani Dana islamiyya, inda ya ce masarautar zata duba yadda zata bada gudun mowa domin shawo kan matsalar Makarantun Addini a Yankin.

KU KARANTA: Mun Shirya Wasanni Ne Domin Tabbatar Da Zaman Lafiya Tsakanin Kabilun Kano — Sakataren SWAN

Ya Kuma yabawa Malaman makarantar saboda gudummawar da suke bayarwa wajen bayar da tarbiyya ga daliban da fatan zasu cigaba.

Shima, Bako Mai jawabi Kuma Malami a Jami ar Bayero dake nan Kano farfesa Usman Abubakar Ibrahim Bichi ya Taya daliban da sukayi saukar murna tare da yin jawabi Mai tsawo akan muhimmancin illimintar da ya’ya mata a cikin al’umma.

Tunda farko Shugaban makarantar Malam Sani Nuhu yace an kafa makarantar a 2014 Kuma ta yaye fiye da dalibai 165 tare da lasafta wasu daga cikin matsalolin dake damun makarantar wadanda Suka Hadar da karancin ajujuwa da bukatar katange makarantar da Kuma matsalar zaizayar kasa a wasu sassan makarantar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *