DAGA: KAMAL UMAR KURNA, Kano.
Kwamitin da Gwamnatin jihar Kano ta kasa domin kwashe Tilin sharar da aka tara a gurare daban-daban a cikin kwaryar birnin Kano ya ce ya kusa kammala aikin sa na debe dukkan Sharar.
Shugaban kwamitin Alhaji Amadu Haruna Zago ne ya bayyana hakan a zantawarsa da wakilin GLOBAL TRACKER a Kano.
Ya ce kwamitin zai kammala aikin sa nan da kwanaki biyu masu zuwa wanda a yanzu aikin nasu na kwashe sharar yana matakin karshe.
KU KARANTA: Tsaftar Muhalli: Kotun Tafi Da Gidan Ka Ta Ci Tarar Mutane 34
Ya ce aikin kwashe shara aiki ne na yau da kullum, kuma idan kwamitin ya kammala aikin sa, maaikatar muhalli ta jihar Kano zata dora daga inda ya tsaya da nufin cigaba da tsaftace jihar.
Shima a nasa jawabin, daraktan ayyuka na hukumar kwashe sharar jihar nan Alhaji Sha’aya’u Abdulkadir Jibrin ya ce rashin isassun kayan aiki ne ya Hana su kwashe sharar tuntuni.
Unguwannin da kwamitin ya kwashe shararsu a yau sun Hadar da Kofar ruwa da Shahuci da Dan dawaki police station da Man ladan da sauran su.