• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Dan Majalisa Ya Biya Kudin Jarabawar NECO ga Dalibai 100

ByGlobal Tracker

Jun 18, 2023

DAGA: IBRAHIM AMINU RIMIN-KEBE, KANO

 

Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomun Minjibir da Ungogo a majalisar wakilai ta kasa Alhaji Sani Adamu Wakili ya biya wa daliban kananan hukumomun Minjibir da Ungogo su 100 kudin jarrabawar NECO.

Shugaban kwamitin da Dan majalisar ya kafa don lalubo wadanda suka fadi Jarabawar Dakta Surajo Suleman ya bayyana cewa, an biyawa daliban kudin jarrabawa ne a sakamakon faduwar da suka yi a Jarabawar gwaji wato Kwalifayin ta shekarar 2023 taron da ya gudanar a cibiyar yada addinin musulinci ta Karamar hukumar Ungogo.

Ya Kara da cewa, kwaminitin nasu ya kewaya dukkanin makarantun dake kananan hukumomun Minjibir da Ungogo domin zakulo daliban maza da mata.

Dan majalisar ya ce tun a lokacin yana yakin neman zaben sa yayi alkawarin bada fifiko ga fanin ilimi da harkokin kiwon lafiya da samar da ruwan sha da kuma gyaran titunan kananan hukumomun.

KU KARANTA: Zamu Yaki Dukkan Matsalolin Da Ke Damun Makarantun Addini a Yankin Mu — Sarkin Bichi

Ya Kara da cewa, akwai bukatar masu ruwa da tsaki na kananan hukumomin Minjibir da ungogo dasu tabbata sun bada hadin kan daya kamata, domin ganin an cimma nasarorin da aka sanya a gaba.

Sani Wakili ya ce zai yi aiki kafada da kafada da gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf da kuma yan majalisun na kananan hukumomun Minjibir da Ungogo dan ganin kananan hukumomun sun ciri tuta a fanin ilimi.

A nasa jawabin, shugabannin jam’iyyar NNPP na kananan hukumomun Minjibir da Ungogo, Abubakar Ibrahim Abubakar da kuma Alhaji Bilyaminu Musa Adamu Bachirawa, sun bada tabbacin cewa zasu aiki da zababban dan majalisar tarayyar a ko wane lokaci.

Wasu daga cikin daliban da suka amfana da tallafin biyan kudin jarrabawar ta NECO, sun bayyana farin cikin su tare da godewa Alhaji Sani Adamu Wakili.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *