• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Mun Kwashe Kaso 90 Cikin 100 Na Sharar Da Aka Jibge A Birnin Kano — Dan-zago

ByGlobal Tracker

Jun 19, 2023

DAGA: KAMAL UMAR KURNA, KANO

 

Kwamitin karta kwana na kwashe sharar jihar Kano yace ya zuwa yanzu ya kwashe kimanin kaso casa’in (90) cikin (100) na sharar da aka jibge a titunan birnin Kano.

Shugaban kwamitin Ambasada Alhaji Ahmadu Haruna Zago ne ya bayyana hakan lokacin da yake zagayen gani da ido kan yadda aikin kwamitin yake gudana.

Dan-zago ya ce kwamitin nasu yana gab da tattara bayanansa na karshe domin Mikawa gwamnati irin aikin da suka gudanar.

KU KARANTA: Nan Da Sa’o’i 48 Za Mu Kammala Kwashe Sharar Kano — Dan Zago

Ya Kara da cewa ya zuwa an dauki shara kimanin tifa dubu daya da dari da takwas (1108) wanda adadin Hakan ya haura tan dubu arba’in da biyu da dari biyu da tamanin (40,280).

Shima a nasa jawabin Mai unguwar Marmara Alhaji Kabiru Sallau da sauran al’ummar da aka zoyarci yankunansu sun bayyana takaicin su bisa yadda tarin sharar yake barazana ga lafiyarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *