• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Da Dumi-Dumi: Mutane 36 Sun Mutu a Wani Rikici a Somalia

ByGlobal Tracker

Jun 21, 2023

Akalla mutane 36 ne suka mutu a wasu tashe-tashen hankula a jihar Puntland da kuma yankin Lower Shabellebiyu da ke ƙasar Somalia.

Likitoci sun ce aƙalla mutane 26 ne suka mutu a wani kazamin fada da aka gwabza a ranar Talata a yankin Garoowe, babban birnin jihar Puntland.

Haka kuma wasu 10 suka mutu bayan wasu bama-bamai da aka sarrafa daga nesa suka tashi a wani ƙauye kudu maso yammacin Mogadishu babban birnin kasar ta Somalia.

KU KARANTA: Shugabannin Afrika na Shirin Sulhunta Rikicin Sudan

Shaidu sun ce mutane da dama ne suka mutu a fashewar bam na farko sannan bam na biyu ya tashi a lokacin da fararen hula da sojoji suka je wajen domin aikin ceto.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *