DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO
Wani Dattijo Mai shekaru 60 da haihuwa Muhammad Musa ya kasance daga cikin daliban da sukayi saukar Alqur’ani Mai girma a Unguwar Mai aduwa cikin karamar hukumar Dala dake arewa maso yammacin Nigeriya.
Muhammad Musa da sauran dattawa abokan karatunsa sun bayyana cewa shekaru ko tsufa ko kuma dawainiyar iyali baya hana su neman Ilimi.
A lokacin da ake saukar, sanannen makamin addinin musuluncin nan a Kano Sheikh Bashir Bakin-ruwa ya bukaci iyaye dasu kara maida hankali wajen tallafawa makarantun addinin musulunci duba da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen samar da alumma ta Gari.
An dai gudanar da saukar ne na daliban makarantar Raudatul kur’an Murattal bangaren Asuba da ummahatu karo na 2 na dalibai 17 wanda ya gudana a farfajiyar makarantar dake unguwar mai Aduwa dake karamar hukumar Dala.
KU KARANTA: Mun Saukar Alkur’ani Sau 200 Don Samun Shugabanni Na Gari — Balarabe Tatari
Bakin Ruwa ya ce marigayi sheikh Abubakar Ramadan shine ya Assasa makarantar domin yada ilimin addini musulunci da samarda mahaddatan alkurani da kuma kara chusa kaunar Annabi sallallah Alaihi wasallam da sahabbansa a zukatan alummar .
Ya bukaci daliban dasu kara zage damtse wajen neman ilimi a fannoni daban daban na rayuwa, domin samun kyakyawar rayuwa a duniya da lahira.