Rundunar jami’an tsaron gabar ruwa ta kasar Amurka, ta ce an gano ragowar tarkacen karamin jirgin ruwan nan na Titan da ya yi nutse zuwa karkashin teku, wanda binciken kwararru ya tabbatar da cewar, karfin igiyar karkashin ruwan ce tarwatsa shi da karfin tsiya, lamarin da yayi sanadin mutuwar baki dayan mutane 5 da ke cikinsa.
Jagoran aikin neman jirgin na Titan da ya bace Rear Admiral John Mauger, ya shaida wa manema labarai cewar, na’urar bincikensu ta fara gano ragowar tarkacen jirgin ne da safiyar jiya Alhamis, a can kasan tekun na Atlantic da nisan kilomita 4, kuma akwai tazarar akalla kafa dubu 1 da 600, tsakanin inda jirgin nutson ya tarwatse da kuma ragowar katafaren jirgin Titanic da suka yi nufin kai wa gareshi, wanda ya nutse fiye da shekaru 110 da suka gabata.
KU KARANTA: Za’a Kara Kudi Idan Yakin Sudan Ya Kai Lokacin Hajji – NAHCON
Musayar bayanai ta katse tsakanin jirgin Titan da jami’ai ne, bayan tafiyar da ya fara zuwa karkashin tekun Atlantic da kimanin sa’a 1 da mintuna 45 a ranar Lahadin da ta gabata wato 18-06-2023 da safe.
Bayan shafe fiye da kwanaki uku ana ta lalube ne kuma, aka gano muhimman sassa guda biyar na jirgin karkashin ruwan, ciki har da jelarsa da kuma bangarori biyu da ke daidaita karfin igiyar ruwa da nauyinsa da jirgin na Titan ke ratsawa.
RFI Hausa