DAGA: KAMAL UMAR KURNA, KANO
Gwamnatin jihar Kano ta ce kwashe sharar dake jibge akan tirin gidan sarkin Kano daura da gidan Dan masani dab da Kofar shiga Makarantar SAS a matsayin Wani muhimmin aiki Wanda zai Kara fito da martabar Kano.
Shugaban kwamitin karta kwana na kwashe sharar jihar nan Alhaji Ahmadu Haruna Zago shine ya bayyana hakan a lokacin da jami’an hukumar kwashe shara ta jihar nan suka yi dirar mikiya a wajen domin gabatar da ayyukansu.
A cewar Dan zago, hanyar zuwa gidan Dan masani da Kofar shiga Makarantar S.A.S wurare ne masu matukar amfani da tarihi ga al’ummar jihar nan, a don haka akwai Samar da kyakkyawan yanayi a wuraren domin samun cikakkiyar tsafta.
KU KARANTA: Mun Kwashe Kaso 90 Cikin 100 Na Sharar Da Aka Jibge A Birnin Kano — Dan-zago
Dan zago daga Nan sai ya bukaci al’ummar dake rayuwa a yankunan dasu kasance masu bin doka da oda ta hanyar Kai sharar su wuraren da hukuma ta tanada domin zubarwa da nufin samarwa da kansu ingantacciyar rayuwa me cike da lafiya da tsafta.