• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Tsohon Dan Wasan Barcelona da Arsenal Cesc Fabregas ya yi Ritaya Daga Kwallon kafa

ByGlobal Tracker

Jul 1, 2023

Tsohon dan wasan tsakiya Arsenal, Barcelona da Chelsea Cesc Fabregas ya sanar da yin ritaya daga kwallon kafa.

Dan wasan mai shekara 36 ya sanar da yin ritayarsa ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Asabar.

“Ina cike da bakin cikin sanar da ku cewa lokaci ya yi da zan ajiye takalman wasan kwallon kafana,” in ji Fabregas.

Ya yi ritaya ne shekaru daya bayan ya sanya hannu a kwantaragin shekara biyu da kungiyar kwallon kafar Como da ke fafata gasar Serie B a Italiya.

KU KARANTA: Mun Shirya Wasanni Ne Domin Tabbatar Da Zaman Lafiya Tsakanin Kabilun Kano — Sakataren SWAN

“Ba bakin ciki ne kawai ba, domin kuwa zan soma aikin horar da ‘yan wasan kwallon kafa a rukunin B da Primavera na Como 1907,” a cewarsa.

Fabregas ya taimaka wa Sifaniya wurin lashe Kofin Duniya, ya dauki kofin Gasar Firimiya sau biyu a Chelsea da kuma La Liga sau daya a Barcelona.

TRT Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *