• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Tsaftar Muhalli: Wata Kungiya Ta Bawa Dan-zago Lambar Girmamawa

ByGlobal Tracker

Jul 2, 2023

DAGA: KAMAL UMAR KURNA, KANO

 

Shugaban kwamitin karta kwana na kwashe sharar jihar Kano Ambassador Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya Sha alwashin cigaba da sadaukar kan sa wajen ganin jihar nan ta samu habaka da Samar da kyakkyawan yanayi domin dacewa da manofofin gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusif.

Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da kungiyar ‘yan asalin jihar Kano masu tsaftar muhalli suka Mika masa shaidar girmamawa bisa namijin da kokarin da kwamitinsa yayi na kwashe sharar dake jibge a wasu yankunan jihar cikin kankanin lokaci.

Zago ya ce tsaftace Muhalli da titunan Kano nada alaka ta Kai tsaye da Samar da ingantacciyar lafiya ga al’umma, a don zai cigaba da bada dukkan lokacin sa wajen kwashe sharar.

KU KARANTA: Muna Tabbatar Da Tsaftar Guraren Da Suke Da Tarihi a Kano — Zago

KU KARANTA: Mun Kwashe Kaso 90 Cikin 100 Na Sharar Da Aka Jibge A Birnin Kano — Dan-zago

KU KARANTA: Nan Da Sa’o’i 48 Za Mu Kammala Kwashe Sharar Kano — Dan Zago

Tun da farko a jawabin sa, shugaban kungiyar Dakta Bala Mohammed ya ce sun baiwa Dan zago shaidar girmamawar ne duba da yadda cikin kankanin lokaci kwamitinsa ya Samar da yanayi me kyau a Mafi yawan titunan jihar nan, a saboda haka ne kungiyar tasu ta amince da baiwa Dan zago matsayin uban kungiyar tasu domin samun nasarar da aka Sanya a gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *