• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Kalubale Biyar Dake Gaban Kano Pillar Bayan Dawowa Gasar Premier

ByGlobal Tracker

Jul 8, 2023

DAGA: AHMED HAMISU GWALE, KANO

Maganar ta gaskiya Kano Pillars tayi abin da ya kamata a ya ba mata na dawowa gasar Premier ta kasa wato (NPFL), domin kuwa a baya wasu sun ta cewa a bar kungiyar ta gwada kwanjinta a inda ta tsinci kanta.

Sai kuma gashi taje gasar ta NNL kuma tayi wasanni da kananan kungiyoyin, har ta samu damar zuwa matakin playoffs kuma kwalliya ta biya kudin sabulu.

Amma ba haka aka soba wai kanin miji yafi miji kyau, ina nufin rashin nasara a wasan karshe da Pillars tayi a hannun Heartland.

Koma dai menene a karshe mai faruwa ta faru, sai a tinkari gaba.

To amma, wanne kalubale ya ke gaban Kano Pillars a kaka mai zuwa?

Na farko: kungiyar na bukatar a yi mata garanbawul a kowanne mataki, dalilin fadin haka shi ne, duk sanda a kace an samu sauyin shugabancin ko wani abu ami kama da haka, yana bukatar yin aiki da wanda ya san za suyi aiki tare, wanda kuma zaiyi biyayya tare da bada gudun mowa don samun nasara.

Na Biyu: shugabancin Kano Pillars na yanzu, dole ya kalli baya, ma’’ana shugabannin da suka gabata, domin ya yi musu godiya da kuma neman shawararsu domin ciyar da kungiyar gaba.

Na Uku: ya tsarin yan wasan kungiyar ya ke yanzu? Tabbas sai anyi duba ga kowanne dan wasa domin dora shi a sikele wanda hakan zai sa a yi adalci ga kowa.

Babu maganar wai wannan dan wasa Dan Kano ne, wannan kuma ba dan Kano ba, kawai a duba cancanta ga duk wanda aka san zai bayar da gudunmawa domin ciyar ba Pillars gaba.

Wannan gabar tana da mahimmanci sosai musamman yadda yan wasa suke taka rawar gani wajen ciyar da kungiya gaba.

Ahmad Hamisu Gwale, Mai bibiyar harkokin wasanni domin gano wani Abu da yake bukatar a yi gyara.

Na Hudu: Musamman yadda a yanzu kowanne lamari yake ta fiya da zamani, tabbas sai an samar da ci gaba da kuma bibiyar bangaren shafikan sada zumunta da kuma bangaren yada labaran Pillars domin kafafen yada labarai suna taka muhimmiyar rawa a wajen cigaban kungiya a gasar premier ta kasa Nigeria.

Magana ta gaskiya bangaren shafikan sada zumunta na Kano Pillars ba sa wani abin da ya kamata, idan aka kwatanta da sauran kungiyoyin Najeriya ko na kasashen waje.

Maganganun da yawa, kuma an san kowa ya san daidai, muddin ba za a cire sarrai da son zuciya ba to babu wani abu da zai gyaru.

Na Biyar: Bari nayi duba kan yadda gwamnatin data gabata ta gudanar da al’’amuranta tsakaninta da Kano Pillars, Magana daya itace tsohowar gwamnatin Kano ita ce silar lalacewar duka wannan hali da Pillars ta shiga.

Domin kuwa Pillars bata samu kulawa mai inganci ba, sakamakon yadda babu wata kulawa da za a nuna a fili wajen bai wa kungiyar goyan baya.

Zan iya tunawa farkon gwamnatin data gabata tsohon gwamna da kansa ya halarci wani wasan Kano Pillars, amma ba a kammala wasan ba ya fice daga filin saboda ihu da magoya bayan kungiyar su kai masa.

Amma dai na lura sabuwar wannan gwamnatin ta Kano sai tayi da gaske domin dawo da marbatar Kano Pillars domin kuwa idan ba ai da gaske ba to akwai sauran tsalle.

Gwamna Abba Kabiru Yusuf da gaske sai kayi abin da ya dace domin dawoda kimar kungiyar da aka santa da shi a shekarun baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *