• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Ziyarar ACOMIN Gabasawa: Zamu Magance Dukkan Matsalolin Da Aka Zayyana A Wata Daya — Garun-Danga

ByGlobal Tracker

Jul 11, 2023

Majalisar karamar Hukumar Gabasawa ta Sha alwashin kawo karshen dukkan Matsalolin da kungiyar dake rajin yaki da cutar zazzabin cizon sauro a Nigeria ACOMIN ta Zayyana a mazabu biyu a yankin cikin wata guda.

Shugaban karamar Hukumar Alhaji Mahe Garba Garun-Danga ne ya bayyana hakan lokacin da wakilan kungiyar ta ACOMIN su kai masa ziyara domin tattaunawa da kuma lalubo yadda za’a Magance kalubalen da Asibitocin yankunan guda biyu ke fuskanta taron da ya gudana a garin Zakirai Shalkwatar Gabasawa.

Garun-Danga wanda Sakataren karamar Hukumar ta Gabasawa Alhaji Ado Musa Zakirai ya wakilta ya ce nauyi ne da ya rataya a wuyan su na ganin an magance matsalar da Asibitocin kauyen Doga dake mazabar Garun-Danga da na Mazabar Yautar Kudu an magance su don kula da lafiyar al’ummar yankin.

“Su kungiyoyin sa Kai kamar su ACOMIN da ma na gaya musu cewa alhakin su ne dukkan aikin da za suyi ya zama sun saka al’ummar yankin a ciki, yanzu misali idan ACOMIN zata Yi musu aikin kula da lafiya na Naira dubu 100, bayan an kammala kuma ya zama akwai wani aikin na naira dubu 20, to su day kansu za suyi kudi-kudi domin gudanar da aikin saboda sunga muhimmancin sa,” inji Zakirai.

KU KARANTA: Mun Shirya Wasanni Ne Domin Tabbatar Da Zaman Lafiya Tsakanin Kabilun Kano — Sakataren SWAN

KU KARANTA: YUMSUK: SUG Ta Roki Karin Adadin Sabbin Daliban Da Ake Duba Lafiyar Su

Sakataren karamar Hukumar daga nan ya bukaci al’ummar yankin musamman masu rike da mukaman siyasa da sarakunan gargajiya da ma sauran al’umma da su rika tallafawa wajen kula da asibitoci da cibiyoyin kula da lafiyar al’umma.

A jawabinsa, jami’in kula da shirin a nan Kano “Programme Officer” Sharif Abubakar ya ce sun kai ziyarar ne domin tattaunawa da shugabancin karamar Hukumar hanyoyin da za’a bi domin magance matsalolin a cibiyoyin kula da lafiyar guda biyu.

Ya ce matsalolin sun hada da Barewar wani bangare na rufin “Ceiling” Asibitin da ke Kauyen Doga a Mazabar Garun-Danga da Kuma matsalar wutar lantarki da Asibitin Yautar Kudu ke fuskanta.

Malam Sharif ya yabawa majalisar karamar Hukumar bisa yadda ta bada tabbacin kammala aikin cikin wata guda.

Ya kuma bukaci al’ummar yankin da ma sauran yankunan jihar Kano da su rika kula da asibitocin dake yankunan su domin ta haka ne zasu cigaba da kula da lafiyar su cikin sauki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *