DAGA: IBRAHIM SANI GAMA, KANO
Kungiyar direbobi tashar Malam Kato dake Kano ta bukaci Gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf da yayi duba tare da kwace tashar Motar da tsohuwar Gwamnatin da ta gabata ta Siyarwa wasu dai-dai kun mutane.
Sakataren kungiyar Alhaji Balarabe Ahmed ne ya bayyana hakan la’akari da yadda tashar ta ke haifar da cunkoson ababen hawa a bakin tashar har zuwa kasuwar bata.
Balarabe Kwankwasiyya ya bayyana cewa direbobin na daya daga cikin mutanen da suka baiwa Gwamnatin mai ci gudunmawa domin ganin an kafa Gwamnatin, amma gashi sun koma yadda suke a Lokacin Tsohon Gwamnan jihar Kano Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso daya Taimakawa kungiyar suka dawo cikin Tashar Malam Kato domin yin amfani da ita.
Ya bayyana cewa, Magidanta da matasa da dama ne ke sana’a a cikin tashar amma sakamakon siyar da tashar da Gwamnatin da ta gabata ta yi asirin wasu da yawa ya tonu saboda sun rasa ayyukan yi.
KU KARANTA: Janye Tallafin Man Fetir: Ku Kwantar Da hankalin Ku Abubuwa Za Su Daidaita — Mamuda Zangon Kabo
A don haka Kungiyar ta kara Tunatar da Gwamnatin jihar Kanon cewa duk da bukatar da Gwamnatin ta yi dakatar da duk wasu gine-gine a guraren dake mallakin Gwamnati amma hakan, ba ta sauya zani ba, domin kuwa ko a jiya sai da ma’aikatan dake Gine-ginen suka ci gaba da aiki.
Balarabe kwankwasiyya ya ce yin hakan kamar karya Umarnin Gwamnatin ne da kuma raina hukunci da yin Fatali da sanarwar da Gwamnatin Injiya Abba Kabir Yusuf ne.
Saboda haka Kungiyar direbobin take kira ga Gwamnati da masu Ruwa da tsaki a Fannin gine-gine da Kwamishinan harkokin sufuri na jihar kano da Shugaban Hukumar KANUPDA da su kaiwa Kungiyar direbobin daukin gaggawa domin fitar da Dunbun Alumma daga cikin Damuwa.
Idon za’a iya tunawa Gwamnati mai ci ta yi kiraye-kiraye da mutane su daina siyan kayan Gwamnati domin hakan ba zai haifar da ‘Da’ mai ido ba.