DAGA: KAMAL UMAR KURNA, KANO
Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Ambasada Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya bayyana bukatar dake akwai na Samar da Wani tsari tsakanin hukumar sa da shugabannin kasuwannin jihar don tsaftace kasuwannin.
Ahmadu Zago ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a kasuwar kantin kwari lokacin da ake gudanar da aikin kwashe sharar wanda shine Karo na 4 a kasa da makwanni 2.
Dan-zago ya ce hukumar sa da gwamnati ba zasu cigaba da zura idanu da yawa daga cikin kasuwannin jihar nan suna cigaba da rufe tituna ba sanadin sharar da suke zubarwa a akan titunan.
KU KARANTA: Zu Mu Samar Da Tsarin Yaki Da Zubar Da Shara Barkatai a Kano — Dan-Zago
KU KARANTA: Tsaftar Muhalli: Wata Kungiya Ta Bawa Dan-zago Lambar Girmamawa
KU KARANTA: Mun Kwashe Kaso 90 Cikin 100 Na Sharar Da Aka Jibge A Birnin Kano — Dan-zago
Wasu daga cikin ‘yan kasuwar ta kwari sun bayyana cewa ana fito da sharar ne daga cikin kasuwar a tsakiyar dare da Kuma unguwar Fagge ta yadda sai dai su wayi gari suga sharar ta toshe hanyar wucewa.
Daga nan ya ce duba da yadda gwamnati take kashe makudan kudade wajen aikin kwashe sharar akwai bukatar al’umma su bada cikakken hadin Kai da goyon baya domin samun nasarar da aka Sanya a gaba.