• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Rasha ta Fasa Tsawaita Yarjejeniyar Fitar Da Hatsin Ukraine

ByGlobal Tracker

Jul 17, 2023

Kasar Rasha ta sanar wa Majalisar Ɗinkin Duniya da takwararta ta kasar Turkiyya da kuma Ukraine cewa ba za ta sake sabunta yarjejeniyar fitar da hatsi ba wadda ta bai wa Ukraine damar fitar da hatsi ta Bahar Aswad.

Mai magana da fadar Kremlin Dmitry Peskov ya ce yarjejeniyar ta kawo karshe a yau Litinin.

Yarjejeniyar dai ta bai wa jiragen dakon kayan abinci damar wucewa ta tekun Bahar Aswad daga tashar jiragen ruwa ta Odesa da Chornomorsk da kuma Yuzhny/Pivdennyi.

To amma Rasha ta ce za ta dawo cikin yarjejeniyar idan aka amince da sharuɗanta.

KU KARANTA: Rasha Ta Karɓi Shugabancin Kwamitin Tsaro Na MDD

KU KARANTA: AU Ta Gamsu Da Shirin Nigeria Na Gudanar Da Sahihin Zabe — Kenyyata

BBC Hausa ta rawaito cewa tun a baya, Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi korafin cewa ba a mutunta wani ɓangare na yarjejeniyar da ya bayar da damar fitar da kayan abinci da kuma taki daga ƙasar.

Ya ce ba a kai kayan hatsi ba zuwa ƙasashe matalauta, wanda yana cikin sharaɗi da aka amince da shi a yarjejeniyar.

Rasha ta sha nanata cewa takunkuman ƙasashen yamma na hana ta wajen fitar da kayan abinci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *