• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Kungiyar Tsofaffun Daliban CAS Ta Taya Adamu Kibiya Murnar Zama Kwamishina

ByGlobal Tracker

Jul 18, 2023

Kungiyar tsofaffin Daliban makarantar share fagen shiga jami a ta Kano wato CAS aji na shekarar 2003 ta gudanar da liyafar cin Abinci domin taya murna ga Daya daga cikin ‘ya’yan kungiyar Adamu Ali Ibrahim kibiya bisa samun mukamin kwamishina a kunshin gwamnatin jihar Kano.

Shugaban kungiyar Aminu kofar mata ya ce sun shirya taron liyafar cin abinci ne domin taya murna ga kwamishinan kasa da Safiyo Adamu Ali Ibrahim kibiya, bisa mukami da Gwamnatin jihar Kano ta bashi, inda ya bayyana sabon kwamishinan a matsayin jajirtaccen matashi wanda yake bada gudunmawa domin cigaban alumma.

Shugaban kungiyar ya kuma yi kira a gare shi daya gudanarda da ayyukansa bisa gaskiya da rikon Amana.

Da yake jawabi, Kwamishinan ya bayyana farin cikinsa bisa wannan karramawa da Abokanan karatun sa suka yi masa, ya kuma yabawa malaman su bisa irin gagarumar gudanmawa da suka basu a lokacin da suke a matsayin dalibai.

KU KARANTA: Muna Roko A Daga Darajar Shafin Intanet na YUMSUK — Shugaban Dalibai

KU KARANTA: Yanzu–Yanzu: Wellcare Ya Nemi Afuwar Gwamnatin Kano Bayan Rufe Shi.

Ya ce mukamin da aka bashi na matasa ne, adon haka yake bukatar yan uwansa matasa dasu taimaka masa ta hanyar bashi shawarwarin da suka da ce da kuma adduoi domin sauke Nauyin da aka dora masa, yadda ya da ce domin hakanne zai taimaka wajen sake baiwa matasa damammaki a cikin kunshin gwamnatin Kano.

A nasa Bangaren, daya daga cikin malaman Dakta Auwalu Mudi Yakasai ya ce babban burin malami da kuma iyaye shine su samar da yaya wadanda zasu samu daukaka fiye da tasu inda yaja hankalinsa da rike gaskiya da amana wajen gudanar da ayyukansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *