• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Tsaftar Muhalli: Zamu Girmama Shawarwarin Yan Kasuwar Kano — Shugaban REMASAB

ByGlobal Tracker

Jul 18, 2023

DAGA: KAMAL UMAR KURNA, KANO

 

Gwamnatin jihar Kano tace zata yi amfani tare da girmama shawarwarin da shugabannin kasuwannin jihar nan zasu bata domin shawo kan tarin shara a cikin kasuwannin da Kuma zubar da ita akan titi ba bisa ka’ida ba.

Shugaban hukumar kwashe shara da Tsaftar Muhalli ta jihar Kano Alhaji Ahmadu Haruna Zago ne ya bayyana hakan lokacin daya karbi tawagar Shugabannin kasuwannin jihar nan wadanda suka kawo masa ziyarar aiki a ofishinsa.

Dan zago ya ce da hadin kan shugabannin kasuwannin ne kadai hukumarsa zata samu nasarar kawar da tarin sharar dake dankare a kasuwannin Kano da wasu titunan jihar nan musamman wadanda suke da makwabtaka da kasuwannin.

KU KARANTA: Muna Kiran Gwamnan Kano Ya Kwato Tashar Malam Kato Da Tsohuwar Gwamnati ta Siyar — Balarabe Ahmed

KU KARANTA: Yan Kasuwa a Ungogo Sun Ta Ya Abba K. Yusuf Murnar Lashe Zabe

Da suke nasa jawaban daban-daban shugabannin kasuwannin wanda shugaban kasuwar Sabon Gari Mohd Bashir Abdul Durumin-iya ya yi bayani a madadin su ya jaddada cewa lamarin shara abu ne me wuyar sha’ani Wanda ya dade yana ci musu tuwo kwarya.

Daga nan sai ya tabbatar da cewa zasu hada kan su waje guda domin marawa kudirin gwamnati baya domin cimma nasarar da aka Sanya a gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *