DAGA: KAMAL UMAR KURNA, KANO
Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirin ta na baiwa kungiyoyi masu zaman kan su na ciki da wajen kasar nan cikakken hadin kan daya kamata domin ciyar da fannin lafiya gaba a jihar nan.
Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif ne ya bayyana hakan a wajen kaddamar da yiwa masu larurar ido da yawansu ya Kai 1, 818 aiki kyauta a asibitin Makka Wanda cibiyar King Salman na kasar Saudiyya ta dauki nauyin yi musu hadin gwiwa da gwamnatin jihar Kano.
Gwamna Yusuf wanda Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar nan Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya wakilta ya ce cibiyar ta king Salman ta jima tana yin irin wadannan ayyuka domin inganta rayuwar masu karamin karfi a fadin duniya baki daya.
KU KARANTA: Tsaftar Muhalli: Wata Kungiya Ta Bawa Dan-zago Lambar Girmamawa
KU KARANTA: Tsaftar Muhalli: Kotun Tafi Da Gidan Ka Ta Ci Tarar Mutane 34
Da yake jawabi a wajen kaddamarwar kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Abubakar Yusif ya ce gwamnatin jihar Kano ce ta dauki nauyin tantance wadanda za’a yiwa aikin ta hanyar hada hannu da gidauniyar domin zakulo wadanda suka dace domin ayi musu aikin kyauta.
Tunda farko da yake nasa jawabin karamin jakadan kasar Saudiyya dake Kano Khalil Ahmad Admawi ya ce King Salman ya amince da gudanar da aikin ne a sassa da yawa na duniya domin taimakawa masu karamin karfi a tsakanin al’umma.