Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya ce hukumar sa zata yi amfani da sashin dokar ma’aikatar wajen tursasawa tare da magance dabi’ar zubar da shara da tsakar dare a wuraren da basu kamata ba a jihar nan.
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai sanda ma’aikatan hukumar suke tsaka da aikin kwashe sharar dake Fagge ‘yan Alluna.
Dan zago ya ce abin takaici ne yadda wasu suke bin tsakar dare suna jibge sharar akan titunan jihar nan da wuraren da basu dace ba musamman wuraren da aka kwashe sharar tun da farko.
KU KARANTA: Zamu Samar Da Tsarin Tsaftace Kasuwannin Kano — Dan-zago
KU KARANTA: Zu Mu Samar Da Tsarin Yaki Da Zubar Da Shara Barkatai a Kano — Dan-Zago
A bayanan su tunda farko mazauna kasuwar ta ‘yan Alluna sun yaba da yadda aikin kwashe sharar yake gudana a fadin jihar nan Koda dai wasu daga cikin su sun bayyana cewa kamata gwamnati ta gudanar da aikin tuntuni.
Daga cikin wuraren da hukumar kwashe sharar tayi aiki a yau sun hada da Fagge ‘yan Alluna da karkashin gadar kasuwar Bata da New Road dake Unguwar Sabon Gari.