• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Yadda Aka Fara Zanga-Zangar Karin Farashin Man Fetur a Edo

ByGlobal Tracker

Jul 24, 2023

Ƙungiyoyin farar hula a jihar Edo sun hau kan titunan Benin, babban birnin jihar, domin nuna adawa da karin farashin man fetur da aka yi a baya-bayan nan.

Masu zanga-zangar sun bi ta wasu manyan tituna suna yin Allah-wadai da karin da kuma tsadar rayuwa a Najeriya.

Masu zanga-zangar dai sun ce abin na ci musu tuwo a kwarya inda suka soki matakin karin farashin man fetur yayin da ake fama da tsantsar talauci.

Masu zanga-zangar na dauke ne da kwalaye masu rubuce-rubuce daban-daban, sun kuma yi watsi da shirin tallafin Naira 8,000 da Gwamnatin Tarayya ke yi shirin yi bayan cire tallafin man fetur ɗin.

KU KARANTA: Zanga-Zanga Ta Barke Sakamakon Cire Tallafin Man Fetir a Angola

KU KURANTA: Janye Tallafin Man Fetir: Ku Kwantar Da hankalin Ku Abubuwa Za Su Daidaita — Mamuda Zangon Kabo

Zanga-zangar ta zo ne makonni bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa an cire tallafin mai. Tun bayan nan kuma farashin kaya da man fetur suke hauhawa a fadin Nigeria.

Yayin da gwamnatin tarayya ke cewa matakin an dauka ne don ci gaban kasa, masu lura da al’amuran yau da kullum na ganin zai jefa kasar cikin mawuyacin hali.

A ci gaba da daukar wannan mataki, gwamnatin tarayya ta bayar da shawarar bayar da tallafin Naira 8,000 ga ‘yan Najeriya amma daga baya ta ce za ta sake duba lamarin bayan sukar da shirin ya sha.

Gwamnati ta yi kira ga ƴan Najeriya su yi hakuri kuma ta ce ana daukar matakan rage radadin cire tallafin.

 

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *