• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Mutane Sama Da 340 Sun Kamu Da Cutar Kwalara a Sudan

BySani Magaji Garko

Sep 20, 2024

Adadin wadanda suka mutu sakamakon barkewar cutar amai da gudawa a Sudan ya kai 348 a cewar ma’aikatar lafiyar kasar.

Barkewar cutar ta shafi jihohi tara, inda sama da mutane 11,000 suka kamu da cutar. Bugu da ƙari, akwai damuwa game da yiwuwar barkewar zazzabi, a wasu yankuna tare da wasu mutane biyu da ake zargin sun mutu wanda suka fito daga iyali daya.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ambaliya sun ta’azzara yaduwar cutar kwalara tun watan Yunin da ya gabata a kasar.

KU KARANTA: Najeriya ta Sake Kwashe ‘yan ƙasar Ta 126 Daga Sudan

Tsarin kiwon lafiya mara inganci a kasar Sudan wanda da yaki ya daidaita ya kara dagula kokarin da ake yi na dakile cututtuka masu yaduwa.

Ministan lafiya na Sudan Haitham Ibrahim ne ya ayyana bullar cutar kwalara bayan shafe makwanni ana ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar da yaki ya daidaita.

Ministan ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ma’aikatarsa ​​ta fitar.

Haitham Ibrahim ya ce an dauki matakin ne tare da hadin gwiwa da hukumomi a jihar Kassala da ke gabashin kasar, da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya, da kwararru bayan “ganowar da dakin binciken lafiyar jama’a na kwayar cutar kwalara.”

Yakin da ake yi yanzu haka tsakanin rundunar sojan Sudan din da dakarun rundunar RSF yayi sanadin raba mutane miliyan 25 daga Muhallinsu.

Rahotanni sun ce jihohin Kassala da El Gezira da kuma Khartoum, babban birnin kasar sune yankin da cutar ta fi yaduwar

TRT Afrika, Aljazeera.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *