Jam’iyar PRP ta ce ta fara aikin Sabunta rejista da kuma yin sabbi ‘yan Jam’iyar a ranar Talata 17 ga Satumbar 2024.
Sakataren Jam’iyar Alhaji Musa Maigari ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aikowa GLOBAL TRACKER a Kano ranar Asabar.
Sanarwar ta ce dukkan ‘ya’yan Jam’iyar da suke son yi musu rejista ko sabuntawa, zasu iya ziyartar Ofishin Jam’iyar dake lamba 6 kan titin AP daura da filin Polo a Kano.
KU KARANTA: Kano: Hanyarmu Ta Zama Barazana Ga Rayuwarmu — Al’ummar Dan-dishe
“Saboda haka jam’iyyar na kira ga wadanda basu riga sunyi ba da su gaggauta yin haka kafin karshen watan nan,” inji Maigari.
“PRP na maraba da sauran jama’a masu sha’awar shiga jam’iyyar da suyi ragista domin samun damar shiga tsare-tsaran jam’iyyar. PRP na so tayi amfani da wannan damar domin kira ga masu son tsayawa takara a zaben kananan hukumomi mai zuwa da su hanzarta cikawa da kuma dawo da forms da suka karba,” inji sanarwar.
Maigari daga nan ya bukaci ‘ya’yan Jam’iyar da su gaggauta ziyartar Ofishin domin yin rejista kafin karshen watan satumbar 2024.