• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

DA DUMI-DUMI: Gwamna Fubara ya Rantsar Da Shugabannin Kananan Hukumomin Da aka zaba

BySani Magaji Garko

Oct 6, 2024

Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara a ranar Lahadi a yau Lahadi ya rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi 23 da aka zaba.

Rantsuwar wacce aka gudanar a zauren majalisar zartarwa na gidan gwamnati dake Fatakwal, babban birnin jihar, ta zo kwana guda bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Ribas ta gudanar da zaben kananan hukumomin jihar.

Gwamnan ya rantsar da sabbin zababbun shugabannin kananan hukumomin, jim kadan bayan da hukumar Zaɓe ta jihar Ribas RSIEC ta ba su takardar shaidar cin zabe.

KU KARANTA: Shugaban Nijar Bazoum Ya Taya Bola Tinubu Murnar Cin Zaɓe

Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa jam’iyyar APP ta lashe kujeru 22 daga cikin 23, yayin da Jam’iyar AA ta lashe karamar hukuma daya a zaben kananan hukumomin da aka gudanar jiya, Asabar.

Shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed da tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa Uche Secondus ne suka halarci rantsuwar.

Akwai Karin bayani….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *