• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Zaben Kananan Hukumomi: Gwamnatin Kano Ta Sanya Dokar Takaita Zirga-zirga

BySani Magaji Garko

Oct 25, 2024

Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro sun sanar da Sanya dokar takaita zirga-zirgar jama’a da ababen hawa a fadin jihar daga karfe 12:00 na daren Juma’a zuwa karfe 6:00 na yammacin ranar Asabar.

Wannan matakin na da nufin tabbatar da an gudanar da zabukan kananan hukumomi cikin kwanciyar hankali da lumana, wanda aka shirya gudanarwa a dukkanin mazabun 484 dake fadin kananan hukumomi 44 na jihar.

Wata sanarwar da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Baba Halilu Dantiye, ya rabawa manema labarai ta ce dokar Zata Fara aiki daga daren yau.

KU KARANTA: DA DUMI-DUMI: Gwamna Fubara ya Rantsar Da Shugabannin Kananan Hukumomin Da aka zaba

Sanarwar ta jaddada kudirin gwamnati na gudanar da sahihan zabe kuma cikin lumana, inda sanarwar ta ce dakatar da Zirga-zirgar bata shafi masu aikin yau da kullum ba.

Kwamishinan ya ja hankalin duk wadanda suka cancanci kada kuri’a da su yi amfani da ‘yancinsu na ta hanyar shiga cikin harkokin zabe domin karfafa dimokradiyya a jihar.

Gwamnati ta bukaci dukkan al’ummar jihar Kano da su bi dokar takaita zirga-zirga domin kare lafiyar jama’a da ingantaccen zabe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *