Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce ta daddale naira 71,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta da za ta biya ma’aikatanta.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a fadar gwamnatin jihar ranar Talata bayan ganawa da wakilan ƙungiyar ƙwadago.
Wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ta ce ƙarin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Nuwamban 2024.
KU KARANTA: Dalilai 7 da Suka sa Kungiyoyin NLC da TUC Fasa Yajin Aiki
Kano ta zama ɗaya daga cikin jihohin da suka amince da biyan sama da abin da gwamnatin tarayya ta amince na N70,000 tun a watan Yuli.
Jihohin Legas da Rivers ne kan gaba bayan sun amince da N85,000, sai kuma Neja da ta ce za ta biya N80,000.
BBC Hausa