• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Za Mu Yi Aiki Tukuru Don Cigaban Al’ummar Dawakin Kudu, Kwankwasiyya — Kabiru Jagora

BySani Magaji Garko

Oct 31, 2024

Sabon Kansila Mai Gafaka na karamar hukumar Dawakin Kudu wato “Supervisory Councilor” Alhaji Kabiru Jagora ya sha alwashin yin aiki tukuru don cigaban karamar hukumar Dawakin Kudu da al’ummar ta dama darikar Kwankwasiyya baki daya.

Kabiru Jagora ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da wakilin GLOBAL TRACKER jin kadan bayan karbar takarar nadi.

Ya ce Ofishinsa zai yi aiki tukuru don ganin an sami kyakykyawar alaka tsakanin majalisar kansilolin yankin da kunshin shugabancin yankin don gudanar da ayyukan raya kasa ga al’umma.

KU KARANTA: Muna Kiran Gwamnan Kano Ya Kwato Tashar Malam Kato Da Tsohuwar Gwamnati ta Siyar — Balarabe Ahmed

“Mu a Dawakin Kudu darikar Kwankwasiyya itace al’ummar yankinmu suke yi, sunyi amannar cewa tana da manufofin cigaban Matasa da al’ummar ba tare da la’akari da inda mutum ya fito ba, saboda da haka zamu tabbatar kowanne dan yankin ya amfana, domin za’ayi mulki na al’umma ne ba na bukatar wani mutum kawai ba,” inji Kabiru.

“Daya daga cikin aikinmu shine zama tsakanin majalisar kansiloli da shugabancin karamar hukumar saboda haka zamu tabbatar an yaukaka kyakykyawar alaka tsakanin bangarorin biyu, saboda mu dama a darikar Kwankwasiyya Uwa-daya, uba-daya muke,” inji Kansilan.

Daga nan ya bukaci al’ummar yankin da su cigaba da goyon bayan shugabanni da yi musu addu’o’i don samun nasarar gudanar da ayyukan raya kasa da cigaban al’umma.

Kabiru Jagora ya kuma yabawa jagoran darikar Kwankwasiyya na kasa Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdusalam Gwarzo da shugaban karamar hukumar Dawakin Kudu Alhaji Sani Ahmed Mai-rago da Matemakinsa Alhaji Shu’aibu Aliyu Yar-gaya da duk sauran masu ruwa da tsaki na darikar Kwankwasiyya a yankin.

Kansilan ya kuma yabawa jagoran darikar Kwankwasiyya na Dawakin Kudu Alhaji Abubakar Aminu Jagaba wanda kuma shine sakataren karamar hukumar bisa yadda yake ayyukan cigaban al’umma.

“Alhaji Aminu Jagaba dan amanar Kwankwaso ne kuma muma horon da ya bamu kenan biyayya ga darikar Kwankwasiyya wacce bata da wata manufa da ta wuce cigaban al’umma, saboda haka zamu cigaba da biyayya sannan da aiki tukuru don cigaban mutanen mu,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *