• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Mun Karbi Yan APC Sama Da 200,000 a NNPP Daga Kananan Hukumomi 11 a Kano — Kwankwaso

BySani Magaji Garko

Nov 12, 2024

Jam’iyar NNPP ta yi nasarar karbar yan siyasa sama da dubu dari biyu (200,000) wanda suka sauya sheka daga Jam’iyar APC mai mulkin Nigeria da suka fito daga kananan hukumomi goma sha daya a Kano.

Mai bawa gwamnan Kano shawara a harkokin siyasa Honarabil Sanusi Suraja Kwankwaso ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da wakilin GLOBAL TRACKER a Kano ranar litinin.

Ya ce mutane da aka karba mafiya yawansu sun fito ne daga yankin Kano ta Arewa wanda nan ne yankin jigo a Jam’iyar APC kuma Matemakin shugaban Majalisar dattawan Nigeria.

KU KARANTA: Zaben Gwamna a Nigeria: Jihohin Da APC, PDP, NNPP Suka Yi Nasara

Acewarsa, wandanda aka karba sun fito ne daga kananan hukumomin Kano ta Arewa, da suka hada da Kunchi da Tsanyawa da Tofa da Bagwai da Rimin Gado da Shanono da Kabo da Gwale da Dala da karamar hukumar Binni da kewaye da kuma Takai.

“A karamar hukumar Kabo, mun karbi matemakin na musamman ga matemakin shugaban majalisar dattawan Nigeria wanda ya bar Jam’iyar APC ya dawo NNPP mai alamar Littafi da Hular neman Ilimi, da kansiloli 7 da shugaban jami’yar APC na karamar hukumar da shugabar Mata ta Kabo da sauran jigajigan APC,” inji Kwankwaso.

“A Kunchi/Tsanyawa kuma, mun Karbi tsohon shugaban Kansilolin yankin, da matemakinsa, da masu rike da mukaman siyasa da yawa. Haka a Rimin-Gado mun karbi tsohon shugaba da matemakin kansiloli dama sauran yan siyasa masu tarin yawa,” inji shi.

Mai taimakawa gwamnan ya cigaba da cewa “a karamar hukumar Takai kuma mun Karbi jigajigan yan siyasa da matemakansu sama da 300 karkashin jagorancin Honarabil Garba Umar Durbunde.”

“Alhaji Dayyabu Maiturare ma daga Dala ya bada gudun mowa sosai, domin karkashin jagorancinsa muka karbi mutane masu yawa wanda suka sauya sheka daga APC zuwa NNPP, haka abin yake a Gwale da ma wasu mutanen da dama.”

Dagane da wandanda suka bar Jam’iyar NNPP kuma, Kwankwaso ya ce hakan ba abin damuwa bane, “idan ka rabi mutane 100 sai kuma ka rasa mutum daya kacal haka bazai zama damuwa ba domin sai da Kwankwasiyya ta rasa wasu jigajiganta sannan ta samu nasarar cin kujerar gwamnan Kano.”

KU KARANTA: Zaben Gwamna a Nigeria: Jihohin Da APC, PDP, NNPP Suka Yi Nasara

“Mun rasa su Yusuf Bello Dambatta, mun rasa su Abba Dabo, da sauran jigajigan, amma kuma mun samu nasarar cin kujerar gwamnan Kano, saboda haka siyasa ta gaji haka,” inji Sanusi.

Sanusi Suraja Kwankwaso ya kuma bayyana gamsuwa da yadda aka gudanar da zaben kananan hukumomin jihar Kano wanda ya bawa Jam’iyar NNPP Nasara a dukkan mazabu 484 na Kano da kujerun shugabannin kananan hukumomi 44.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *