DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO
Daya daga cikin fitattun malaman Addinin Musulunci a jihar Kano dake Arewacin Nigeriya Barrista Habibu Dan-almajiri ya ja hankalin ma’aurata musamman Iyaye Maza da su rika tsara iyalan da zasu iya daukar Nauyinsu domi ‘ya’ya kiwo ne Allah ya bayar kuma zai yi tambaya akan abun da ya bayar.
Sheikh Dan àlmajiri ya bayyana hakan a yayin da yake amsa tambayoyi a cikin shirin zamantakewa wanda yake maida hankali wajen warware Matsalolin da suka shafi rayuwar alumma don lalubu bakin zaren domin tsira a duniya da lahira.
A yayin da yake amsa tambayar wata mata da ta bayyana cewa mahaifin ta ya ce bazai iya basu ci da sha ba alhalin yana da halin hakan inda ya ce kowacce daga cikinsu ta je ta samarwa da kanta abunda zata dinga gudanar da rayuwarta dashi, Malamin ya ce wasu daga cikin iyaye suna bada gagarumar gudunmawa wajen lalacewar yayansu mata ta hanyar gaza sauke nauyin da Allah subhanahu wa ta’ala ya dora musu na ci da sha da basu tarbiyya kamar yadda addinin musulunci ya tanada da sauran bukatu na yau da kullum.
KU KARANTA: Mun Karbi Yan APC Sama Da 200,000 a NNPP Daga Kananan Hukumomi 11 a Kano — Kwankwaso
Malamin ya bayyana bacin ransa game da yadda wasu iyaye suke taimakawa wajen lalacewar yayansu mata, ta hanyar gaza sauke harkokinsu da ya rataya a wuyansu, wanda yin hakan bai dace ba.
Ya bukaci iyaye da kowa ya dubi irin damar da take hannunsa wajen tsara yadda ya kamata ya gudanarda da rayuwarsa da ta iyalansa gwargwadon samunsa domin gujewa fadawa cikin nadama.
Ya ce addinin musulunci addini ne da ya tsara yadda kowa zai gudanar da rayuwarsa ba tare da ya shiga cikin halin kunci ba.
Ya ce ‘ya’ya suna da hakki na wajibi akan iyayensu wanda ya zama wajibi su sauke domin samun ingantacciyar alumma.