Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta yi gargaɗin cewa akwai jabun maganin malaria (Artemether + Lumefantrine 20/120) da yake yawo a kasuwa.
NAFDAC ta bayyana haka ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na X ranar Alhamis, inda ta ce wani kamfani daga Indiya ne mai suna Strides Arcolab Limited, ya samar da maganin.
“An gano maganin na jabu a babban birnin tarayya Abuja da jihar Ribas yayin aikin sa ido na jami’an mu,” in ji sanarwar NAFDAC.
KU KARANTA: NAFDAC Ta Gargadi ‘yan Nijeriya Kan Lemon Kwalba Na Sprite
Ta ce binciken da ta yi a ɗakin gwaje-gwaje kan maganin ya nuna cewa ba shi da inganci. Kuma akwai kura-kurai kan yadda aka yi rubuta a jikin kwalin maganin na jabu.
Hukumar ta ce maganin ya daina aiki kuma lambar rijistar NAFDAC da ke jikinsa ita ma ta bogi ce.
Don haka hukumar ta yi gargaɗin cewa jabun maganin na da illa ga lafiyar ɗan’adam, saboda ba shi da ingancin da ya kamata.