DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO
Jami’ar Khalifa isyaku Rabiu khairun dake jihar Kano a Arewa maso yammacin Nigeriya ta karrama Dalibar da ta samu Nasarar lashe gasar musabakar alkurani ta duniya wato malama Hajara Dan Azumi, yar asalin jihar Gombe.
Jami’ar ta ce ta da kyaututtuka daban daban domin karawa Malama Hajara kwarin gwiwa game da irin bajintar da ta yi na samun nasarar a gasar.
Shugaban jami’ar Farfesa Abdurrashid Garba ya ce jamiar ta karrama Malama Hajara Dan Azumi ne kasancewar ya na daga cikin manufofin kafa ta na karfafawa makaranta alkurani gwaiwa a duk inda suke a fadin duniya, wanda hakan ne yasa suke da tsangaya ta musamman wacce take kula da harkokin alkur’an, wanda wajibi ne kowanne dalibi dake makarantar sanin wani Abu daga alkurani mai girma.
KU KARANTA: NAFDAC Ta Yi Gargaɗi Kan Jabun Maganin Malaria
Farfesa Abdurrashid ya ce babbar burin Khalifa sheikh Isyaku Rabiu shine habbbaka karatu alkurani da sauran ilimi daban daban na rayuwa wanda hakan zai taimaka wajen samun ingantacciyar alumma.
Shima a nasa jawabin, shugaban sashin dake kula harkokin alkur’an da ingantashi na jamiar ta KHAIRUN Barrista Habibu Muhammad Dan-àlmajiri ya ce sun karrama malama Hajara ne a makarantar domin sauran dalibai suyi koyi da irin jajircewar da ta yi, daya bata nasara a cikin rayuwarta.
A karshe Malama Hajara Dan-azumi ta yabawa jami’ar bisa karramawar da sukayi mata ta kuma yi addu’a ga mamallakin jamiar marigayi Khalifa sheikh Isyaku Rabiu bisa gudunmawar da ya baiwa alkur’ani.