A dai-dai lokacin da ake cigaba da kirga kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasar, Dan takarar Jam’iyar NPP mai mulkin kasar Ghana Mahamudu Bawumia ya amince da shan kayi a Zaɓen.
A wani jawabi da ya yiwa manema labarai, mataimakin shugaban kasar ya amince cewa Jam’iyar adawa ta NDC wacce tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama ke yiwa takara ta samu nasara da gagarumin rinjaye.
”Kuma bisa ga bayanan da muka tattara daga cibiyoyin tattara sakamakonmu sun nuna cewa tsohon shugaban ƙasarmu, wanda ke takara a jam’iyyar NDC, John Dramani Mahama ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da gagarumin rinjaye”, in ji Bawunia.
KU KARANTA: Ana Shirin Binne Dan Wasan Ghana Chiristian Atsu
Haka kuma, a sakamakon Zaɓen da hukumar Zaɓe ta kasar ta fitar ya nuna cewa yan majalisar dattawan kasar kuma masu rike da mukaman manyan ministoci hudu (4) sun yi rashin nasara.
Ministocin dai sun hada da ministan cikin gida da na kafiya da na yawon bude Ido wanda babbar kujera ce a kasar da kuma ministan sadarwa.
Ministan yawon buɗe idanu na ƙasar Ghana, Andrew Egyapa Mercer ya faɗi zaɓen kujerarsa ta ɗan majalisar gundumar Sekondi da ke jihar Wester Region.
Andrew – wanda ke cikin jiga-jigan jam’iyyar NPP mai mulki – ya sha kaye a hannun ɗan takarar jam’iyyar NDC mai hamayya.
Andrew Mercer ya kasance ‘yan majalisar gundumar Sekondi tun 2016.
Ga sakamakon mazaɓar da hukumar zaɓen ta bayyana:
Andrew Egyapa Mercer (NPP) – 11,084
Blay Nyameke Armah (NDC) – 14, 558
A jawabinsa na muranar lashe zaɓen, Blay Nyameke Armah na NDC ya gode al’ummar mazaɓar Sekondi bisa nasarar da ya samua a zaɓen tare da alƙawarta sake gina gundumar.
Shima, ministan lafiyar Ghana, Dakta Bernard Okoe Boye ya kasance na baya-bayan nan da ya rasa kujerarsa ta majalisa.
Dakta Boye ya sha kaye a hannun ɗan takarar jam’iyyar NDC mai hamayya, Ayiku Benjamin Narteh.
Ga sakamakon da hukumar zaɓn ta bayyana:
Dr Bernard Okoe-Boye (NPP) – 19,866
Ayiku Benjamin Narteh (NDC) – 23,913
Hakazalika, ita ma, daya daga cikin ƙusoshin gwamnatin Akufo-Addo, Ursula Owusu-Ekuful ta rasa kujerarta ta ‘yar majalisar dokokin ƙasar daga gundumar Ablekuma ya Yamma ta jihar Greater Accra.
Ministar sadarwar ta sha kaye a hannun ɗan takarar jam’iyyar NDC mai hamayya, Reverend Kweku Addo.
Ms Ursula – wadda ta kwashe shekaru takwas tana riƙe da muƙamin ministar sadarwa – ta kasance ɗaya daga cikin kusoshin gwamnatin NPP.
Haka ma Daya daga cikin jigajigan gwamnati Mai barin Gado kuma Ministan cikin gida Henry Quartey na jam’iyyar NPP mai mulki ya rasa kujerarsa ta ɗan majalisar gundumar Ayawaso ta Tsakiya.
Kafin naɗa shi muƙamin ministan, Mista Quartey shi ne ministan jihar Greater Accra.
Ɗan takarar jam’iyyar NDC mai hamayya, Abdul Rauf Tubazu ne ya kayar da shi a mazabar tasa, kamar yadda sakamakon da hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana ya nuna.
Ga yadda sakamakon hukumar zaɓen ƙasar ya nuna:
Henry Quartey (NPP) – 23,345
Abdul Rauf Tubazu (NDC) – 29,755
Charles Kwame Adams (NDP) – 163.
Jim kaɗan bayan bayyana sakamakon zaɓen gundumar, ɗan takarar NDC da ya yi nasara ya ce tuni dama yana da ƙwarin gwiwar lashe zaɓen.
BBC da sauran Kamfanoni Dillancin labarai.