DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO
Majalisar Shura ta darikar Tijjaniyya ta kasa a madadin daukacin mabiya darikar Tijjaniyya sun yabawa gwamna jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa nadin da ya yiwa Sakataren Majalisar Shura ta Darikar Tijjaniyya Barrista Imam Sheikh Habibu Muhammad Dan Almajiri a Matsayin shugaban Hukumar Zakka da Hubusi ta Jihar Kano.
Shugaban majalisar Khalifa Sheikh Sani Shehu Maihula a wata tattaunawarsa da wakilin GLOBAL TRACKER a Kano ranar Juma’a.
Ya ce hakika an ajiye kwarya a gurbinta, inda ya bayyana barrista Dan àlmajiri a matsayin jajirtacce wajen gudanar da ayukansa ba tare da nuna gazawa ba.
KU KARANTA: Gaskiya Ita ce Babbar Siffar Mumini — Barista Dan-almajiri
Shugaban ya kuma bukaci gwamnatin jihar Kano data bashi dukkan goyan bayan da ya dace domin ganin ya dawo da martaba hukumar, kasancewarsa gogagge wanda ya saba gudanarda da muamaloli da mutane daban daban a fannoni na rayuwa.
A karshe yayi addua ga barrista Dan-almajir ya kuma yi masa fatan sauke nauyin da aka dora masa da kuma neman taimakon ubangiji a yayin gudanarda ayyukansa.