• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Makarantar Madinatul Ahbabu Daiba Ta Yi Sauye-Sauye a Shugabancinta a Kano

BySani Magaji Garko

Dec 21, 2024

DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO

A kokarinta na ganin ta kara bunkasa ayyukanta Makarantar madinatul Ahbabu Daiba dake unguwar Rijiyar lemo cikin karamar hukumar Dala a jihar Kano ta gudanar da suye sauye a kunshin shugabancinta na rassa daban-daban dake fadin jihar nan, da kuma Kasa baki daya sakamakon rasuwa da wasu daga cikin shugabanni suka yi da sauyin wajen aiki.

Shugaban makarantun na kasa Khalifa sheikh Ahmad Muhammad Dan-almajir ya ce sunyi hakanne domin maye gurbin wasu daga cikin darakatocin makarantar wadanda Allah yayiwa rasuwa a watannan dasu gabata, da wadanda suka samu sauyin wajen aiki domin cigaba da gudanar da ayyukan makarantar kamar yadda marigayi sheikh Muhammad Dan àlmajiri ya kafa ta.

Khalifa Ahmad Dan almajir ya ce babban burin makarantar shine samar da mahaddata Alkur’ani mai girma da kuma basu ilimi da Tarbiyya.

KU KARANTA: Rasha Ta Karɓi Shugabancin Kwamitin Tsaro Na MDD

Shima a nasa jawabin, Darakta janar na makarantar Malam Ibrahim Abdulaziz ya ce makarantar tana da rassa daban daban a fadin kasar nan wadanda suka kai kimanin dari uku da suke samar da mahaddata Alkur’ani da ilimin addinin musulunci karkashin kulawar Khalifa sheikh Ahmad Muhammad Dan almajir.

Da yake karin haske a a game da sauye sauye da aka gudanar, Barrister Habibu Dan-almajir Fagge ya bukaci sabbin Daraktocin makarantun dasu cigaba da gudanar da ayyukansu bisa gaskiya da rikon amana, wanda hakan shine babban abunda ya sanya makarantar tayi fice wajen samar da mahaddata Alkur’ani wadanda ake alfahari dasu a ko ina.

Ya kuma yi addua ga marigayi sheikh Muhammad Dan almajir da dukkanin daliban sa wadanda suka gabata bisa irin gagarumar gudunmawar da suka bayar domin kafa makarantar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *