Sabon shugaban riko na kungiyar daliban Hausa a kwalejin ilmi ta Aminu Kano AKCOE hadin gwiwa da jami’ar tarayya da ke Dustin-ma a jihar Katsina FUDMA ya ce zasu bada gudun iya karfinsu don cigaban Harshen Hausa da makarantun guda biyu.
Abubakar Sabo ya bayyana hakan ne Jim kadan bayan zaben sa a matsayin shugaban Kungiyar daliban wanda ya kasance na farko a tarihi.
Kwamared Abubakar Sabo ya ba da tabbacin yin aiki tukuru, tare da dukkannin shugabannin kungiyar, domin samar da duk wani cigaba a tafiyar kungiyar.
KU KARANTA: Makarantar Madinatul Ahbabu Daiba Ta Yi Sauye-Sauye a Shugabancinta a Kano
Ya kuma nemi hadin kan sauran wadanda suka nemi takara amma ba su sami nasara ba dama ragowar daliban makarantar na sashin Hausa, da su ba da hadin kai wajen cigaban kungiyar da Kuma ganin kara bunkasar harshen na Hausa a fadin Duniya.
A jawaban su daban-daban shugaban kwamitin samar da kungiyar tare tabbatuwar shugabannin rikon d
Dakta Magaji Ahmad Gaya da sakataren sa Malam Ahmad Mikha’il sun ja hankalin sabbin shugabannin rikon da su zama masu juriya da hakuri tare da gaskiya da rikon Amana don samar da cigaban kungiyar wajen ganin ta je duk in da ya kamata ta je.
An dai zabi Abubakar Sabo a matsayin shugaban riko sai Rabi Ahmad mataimakiyar shugaba da Abdulmusawwir a matsayin magatakarda da sauran mutane goma sha biyu, a mukamai daban-daban.