Gwamnatin jihar Kano ta ce an Sauya lokacin Tsaftar Muhallin da ake Gudanarwa a duk juma’a da Asabar din karshen wata ta Watan Janairun 2025 zuwa mako mai zuwa.
Daraktan yada labarai na maaikatar Muhalli da yaki da sauyin yanayi na jihar Kano Malam Ismail Garba Gwammaja ne ya sanar da hakan a madadin kwamishinan ma’aikatar Dakta Dahiru Muhammad Hashim.
Idan Za’a iya tunawa a shekarun baya ana gudanar da Tsaftar Muhallin a duk juma’a da Asabar din karshen wata koda kuwa ranakun sun sami bambancin mako kamar yadda aka samu a wannan lokacin, Amma a wannan lokacin sai kwamishinan Ya bada umarnin gudanar da Tsaftar Muhallin a mako mai zuwa wanda juma’a zata kasance 31 ga Watan Janairu yayin da Asabar zata kasance 1 ga Watan Fabarairun 2025.
KU KARANTA: Tsaftar Muhalli: Zamu Girmama Shawarwarin Yan Kasuwar Kano — Shugaban REMASAB
Kwamishinan ya bukaci hadin kan dukkan masu ruwa da tsaki don samun nasarar shirin.
A wani cigaban labarin kuma, gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin hada hannu da Kungiyar likitoci ta Kasa reshen jihar Kano da nufin kawo sauyi a bangaren kula da Muhalli.
Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli da yaki da matsalolin sauyin yanayi na jihar Kano Dakta Dahiru Mohammed Hashim ne ya furta hakan lokacin da yake karbar Kungiyar likitoci ta Kasa reshen jihar kano Wanda suka kawo masa ziyara a offishin sa.
Dahiru Wanda ya danganta alakar Muhalli da ciwon lafiya yace alaka ta kusa da kusa wacce Kuma ko wanne bangare yana bukatar daya bangaren domin tafiyar da aikin sa yadda ya kamata.
Ya Kuma bayyana farin cikin sa da wannan ziyarar inda yayi alkawarin yin aiki tare da wannan kungiya a matsayi ta na jigo a bangaren Muhalli da sauyin yanayi, yace kofar sa a bude take domin karbar shawarwari game da abin da zai kawo wa Kano ci gaba cikin sauri.
Kwamishinan wanda yayi dan tsokaci kadan dangane da irin gudure – guduren da yake dasu da nufin kawo sauyi Mai ma’ana da samar da kundi Wanda zai fassara aikace aikacen wannan ma’aikata dama tanade tanaden dokar Muhalli a wani bangare na dawo da jama’a kan hanyan a bangaren Muhallin.
Cikin wata sanarwa da Ismail Garba Gwammaja ya aikewa manema labarai, kwamishinan ya kara da cewa tuni shirye – shirye sun yi nisa wajen samar da jadawali Wanda zai zama al Qibla wajen tafiyar da harkar Muhalli da kula da sauyin yanayi a jihar kano.
Da yake nasa jawabin tun da farko shugaban Kungiyar likitoci ta Kasa reshen jihar kano Dr. Abdulrahman Ali yace sun kawo wannan ziyara domin taya danuwan su murna da Kuma yi masa fatan alheri sakamakon nada shi da gwamna Alh. Abba Kabir Yusuf yayi a matsayin Kwamishina, tare da jadda da goyon bayan su wajen yin aiki kafada da kafada don ciyar da jihar kano gaba.
Dr. Abdulrahman ya Kara da cewa a matsayin su na likitoci tabbas suna da babbar gudummawa da zasu iya bayarwa a bangaren na Muhalli saboda alakar sa da kiwon lafiya, ya Kuma jinjinawa gwamnatin Kano saboda zakulo daya daga cikin su, aka bashi wannan mukamin, Wanda yace tabbas anyi abin da ya dace idan akai la’akari da kwazon sa.