• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Nigeria da Kasashen Duniya 19 da Tsuke Bakin Aljihun Amurka Zaifi Shafa

BySani Magaji Garko

Jan 31, 2025

Sa’o’i kadan bayan rantsar da shi, sabon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanya hanu a kan dokar dakatar da dukkan tallafin da kasarsa take bawa kasashen duniya ba tare da amfanar tallafin ta kai staye ba.

Cibiyoyin bibiya da ba da tallafi sun bayyana cewa Amurkan ta bada tallafi da ya kai dala biliyan 60 a shekarar 2023.

Kasar Ukraine ce a kan gaba a jerin kasashe 20 da suke samun tallafi daga Amurka kuma masana na ganin sune kasashen da tsuke bakin Aljihun da shugaban Amurka Donald Trump yayi zai fi shafa.

KU KARANTA: Zan Haramta Wa Duk Yaran Da Aka Haifa A Amurka Izinin Zama Yan Kasa — Donald Trump

A 2023 Ukraine ta karbi tallafin kusan dala biliyan 14 da rabi daga hukumar bunkasa kasashe masu tasowa ta kasar Amurka USAID.

Jordan ce ta biyu a tallafin kudaden na Amurka inda ta karbi dala miliyan 770 sai Yemen mai kusan dala miliyan 360 yayin da Afghanistan ta karbi dala miliyan 332.

A tallafin kayan yaki kuma Israel ce ke kan gaba.

Ga jerin kasashe 20 da tallafin da Amirka ta basu a 2023:

Ukraine: $16.62bn

Israel: $3.31bn

Ethiopia: $1.77bn

Jordan: $1.72bn

Egypt: $1.45bn

Afghanistan: $1.27bn

Somalia: $1.21bn

Nigeria: $1.01bn

DRC: $0.98bn

Syria: $0.9bn

Kenya: $0.89bn

Yemen: $0.83bn

South Sudan: $0.79bn

Uganda: $0.71bn

Colombia: $0.71bn

Mozambique: $0.66bn

Tanzania: $0.65bn

Lebanon: $0.64bn

Iraq: $0.59bn

Bangladesh: $0.55bn.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *