• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Yakin Rasha Da Ukraine: A Shirye Nake Na Tattauna Da Putin — Zelensky

BySani Magaji Garko

Feb 5, 2025

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce a shirye yake ya tattauna da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kai tsaye matukar hakan zai kawo karshen yakin da kasarsa take yi da Rasha kusan shekaru uku.

Zelensky ya bayyana hakan a wata tattaunawa da manema labarai.

Sai dai mista Zelensky ya ce dole ne tattaunawar ta kunshi kasashen yammacin duniya da Amurka da Rasha da kuma Ukraine.

KU KARANTA: Rasha ta Fasa Tsawaita Yarjejeniyar Fitar Da Hatsin Ukraine

Wannan na zuwa ne kusan wata guda bayan sabon shugaban Amurka Donald Trump ya kama aiki, inda ko a yakin neman zabensa ya sha nanata cewa zai kawo karshen yakin na Ukraine a cikin kwana guda, ko da yake masu sharshi sunyi shakku akan hakan.

Lamarin dai na zuwa ne dai-dai lokacin da kasar Amurka ta dakatar da bawa Ukraine makamai domin yakar tsohuwar uwar gijiyarta wacce aka cire ta a cikinta wato Tarayyar Soviet wacce yanzu ta zama Rasha bayan ballewar wasu kasashe ciki harda Ukraine din.

To sai dai Shugaba Zelensky ya sake nanata bukatarsa ta Karin tallafin makamai daga kasashen yamma domin cigaba da gwabza fada da Rashar.

Ko a watan disambar 2024 sai da GLOBAL TRACKER ta yi hasashen kawo karshen yakin Ukraine a cikin wata guda da rantsar da gwamnatin Donald Trump.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *