• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Mun Yi Amfani Da Ababen Fashewa Masu Nauyin Tan 80 Don Kashe Shugaban Hezbollah — Ministan Isra’ila

BySani Magaji Garko

Feb 7, 2025

Tsohon ministan tsaro na kasar Isra’ila Yoav Gallant ya ce sun yi amfani da Ababen Fashewa da nauyin su ya kai tan 80 don kai harin da ya kashe shugaban kungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah.

Yoav Gallant ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da gidan Talabijin na kasar wato “Israel Channel 12.”

“Bayan mun gama samun bayanan sirri na inda yake sai na umarci jami’an tsaron da dukkan kwamandoji cewa su tabbatar anyi nasara a harin, harma da tambaye su tan nawa na Ababen Fashewa kuke bukata sai suka ce 40 ya Isa, sai ni kuma na ce su tafi da karin 80 don a tabbatar anyi nasara,” inji Ministan.

KU KARANTA: Mutane 7 Sun Mutu a Zanga-zangar Bayan Zaɓe a Mozambique

“Mun kashe shi ne ranar Juma’a, babban hafsan tsaro da kwamandan da ya jagoranci kai harin da sauran kwamandoji ne suka zo min da labarin game da inda aka same shi da kuma dukkan abinda ya faru, sai na tambaye su meye tabbacin an kashe shi, sai suka ce bayanan sun da kaso 90 cikin 100 sun tabbatar da cewa ya mutu a harin,” inji Gallant.

dan za’a iya tunawa GLOBAL TRACKER ta kawo muku rahoton yadda kasar Isra’ila ta ce ita ta kai hari tare da kashe Nassan Nasrallah, harin da kasar Iran da sauran kungiyoyi kawayen ta a Syria, Yemen da sauran su suka yi Allah wadai da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *