• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Jami’ar Bayero Na Shirye-shiryen Yaye Dalibai Karo 39, Karrama Fitattun Mutane

BySani Magaji Garko

Feb 10, 2025

Jamiar Bayero Kano zata gudanar da bikin yaye dalibai karo na 39 da kuma karrama wasu fitattun mutane bisa irin gagarumar gudunmawar da suke baiwa ilimi da kuma cigaban al’umma.

Shugaban jami’ar Farfesa Sagir Abbas shine ya bayyana hakan a yayin da yake ganawa Manema labarai.

Ya ce a rana ta farko jami’ar zata yaye dalibai wadanda suka kammala digiri na farko da kuma karamar diploma da suka kai kimanin mutane 4,402 da suka fito daga tsangayu goma sha daya (11) dake jami’ar.

KU KARANTA: Zamu Yaki Dukkan Matsalolin Da Ke Damun Makarantun Addini a Yankin Mu — Sarkin Bichi

Farfesa Sagir ya ce a rana ta biyu jami’ar zata yaye dalibai masu digiri na biyu da adidinsu yakai kimanin mutane 2,590 sai kuma masu digiri na uku da suka kai mutane 275.

Ya ce taron zai maida hankali ne wajen kara wayar da kan al’umma da sauran dalibai mihimmanci amfani da fasaha domin dogaro da kai inda za a gabatar da bayanai daga malamai daban daban.

A karshe kuma jama’ir zata karrama Tsohon gwamnan soja kanar Sani Bello da digirin girmamawa wanda shine ya samarda sabin mazaunin jamiar sai kuma Alhaji Auwalu Rano wanda shima za a bashi digirin girmamawa bisa irin gudunmawa da yake baiwa daliban suka fito daga yankunan Rano da kibiya da kuma Bunkure ta hanyar biya musu kudin makaranta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *