• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Manoma Na Fargabar Cigaba Da Asara Sakamakon Karancin Ruwa a Kano

BySani Magaji Garko

Feb 10, 2025

DAGA: SHU’AIBU SANI BAGWAI, KANO

Biyo bayan karancin ruwa da ake samu a gonakin Noman rani, Manoma a wuraren noma na Madatsar ruwa ta Watari da ke karamar hukumar Bagwai a jihar Kano sun bayyana fargabar ci gaba da fuskantar mummunar asara sakamakon karancin ruwan noma a gonakinsu fiye da shekaru 3 da suka gabata.

Shugaban Kungiyar Manoman yankin, Alhaji Ibrahim Sani Jan-ruwa ya bayyana haka lokacin da yake nunawa manema labarai wuraren da matsalar ta shafa.

Jan-ruwa ya ce a shekaru 3 da suka gabata Bankin bunkasa harkokin addinin Musulunci na duniya ya bayar da tallafin kudi domin fadadawa da kuma gyara hanyoyin ban ruwa a yankin na Watari amma abun takaici wadanda aka damka al’amarin a hannunsu suka nuna son zuciya da cin amana wajen bayar da aikin ga Dan kwangilar da ba shi da kayan aiki, sakamakon haka ya aiwatar da aiki mara inganci wanda maimakon a sami cigaba sai aka sami koma baya mara adadi.

KU KARANTA: Mun Karbi Yan APC Sama Da 200,000 a NNPP Daga Kananan Hukumomi 11 a Kano — Kwankwaso

Shugaban Kungiyar ya ce a lokacin yarjejeniyar aikin an cimma matsayar cewar cikin watanni 6 Dan kwangilar zai kammala aikin amma sai da ya kwashe fiye da shekaru 3 bai kammala ba, kuma zai rika karbar shawara daga manoman amma suka yi biris da ka’idojin yarjejeniyar saboda suna son su yi aiki mara inganci.

Ya ce sakamakon matsalar ne yanzu haka a kalla gonaki fiye da dubu 10 ba sa samun ruwan amfani wanda hakan babbar barazana ce ga zaman lafiya da cigaban tattalin arzikin jihar Kano.

Ya kara da cewa yanzu haka kiyasi ya tabbatar da cewa kaso daya ne kawai cikin kaso 4 na adadin gonakin manoma ke samun ruwan amfani.

Shugaban Kungiyar ya bukaci hukumomi da kungiyoyin da abun ya shafa su duba wannan matsalar domin kaucewa fadawa cikin mummunan karancin abinci da rashin aikin yi a yankin da Jihar Kano da ma Kasa baki daya bisa la’akari da gudunmowar da Madatsar ruwa ta Watari da ke Bagwai ke bayarwa wajen samar da abinci da ayyukan yi a Kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *