• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Dan Jarida Ya Rubuta Littafin Fassarar Sunayen Hukumomin Gwamnati Da Masu Zaman Kansu

BySani Magaji Garko

Feb 11, 2025

Muhammad Adamu Abubakar, na gidan rediyon tarayya Pyramid FM, Kano ya rubuta littafin fassarar sunayen hukumomin gwamnati da masu zaman kansu da yakamata yan Jaridu da sauran al’umma su yi amfani da shi.

Adamu wanda Edita ne a gidan radiyon tarayya Pyramid ya ce an rubuta littafin ne domin tallafawa al’umma da hukumomi wajen sunayen hukumomi da Hausa.

Kwafin Littafin.

Muhammad ya ce Littafin ya kunshi sunayen hukumomin da ma’aikatun gwamnatin da ma masu zaman kansu da kuma fassarar sunayen zuwa Hausa don amfanin wanda zai taimakawa yan Jarida da masu fassara a ayyukansu na yau da kullum.

KU KARANTA: Mun Karbi Yan APC Sama Da 200,000 a NNPP Daga Kananan Hukumomi 11 a Kano — Kwankwaso

“Mun rubuta wannan Littafin ne don amfanar abokan aikin mu masu tasowa musamman a harkokin fassara daga Turancin Ingilishi zuwa Hausa da ma sauran su,” marubucin ya fada.

Muhammad Adamu ya kuma bukaci masu fassara musamman yan Jarida da su kasance masu yin amfani da Littafin wanda zai taimaka wajen cigaban aikinsu baki daya.

Ya kuma bayyana cewa akwai na sunayen kungiyoyin kwararru da sauransu kuma littafin za’a dinga fadada shi da zarar bukatar hakan ta taso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *