DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO
Jami’ar Bayero ta gudanar da bikin yaye dalibanta karo na 39 da adadinsu ya kai 4,402 da kuma karrama wasu fitattun mutane da suke bada gudunmowa domin cigaban al’umma.
Daliban da aka yaye sun fito ne daga tsangayun 11 dake jami’ar wadanda suka hadar da tsangayar koyar da harkokin addinin musulunci, da kuma tsangayar koyan aikin jarida da tsangaya ilimin kere kare da fasahar sadarwa, da tsangayar ilimin likita da fasahar hada mugunguna da sauaran su.
Da yake jawabi shugaban jami’ar ta Farfesa Sagir Adamu Abbas ya ce babban abunda jami’ar ta sanya a gaba shine bunkasa harkokin ilimi, da fadada buncike da kimiyya da fasaha da samar da ingantaccen ilimi ga al’ummar kasar nan.
KU KARANTA: Sanannen Dan Siyasa, a Kano, Dan Zago Ya Rasu
Sagir Adamu Abbas ya ce jami’ar zata maida hankali wajen bunkasa harkokin fasahar zamani domin samarwa dalibai ayyukan da zasu zama masu dogaro dakawunsu .
Ya kuma bukaci daliban da suka kammala karatunsu a bangarori daban-daban da suyi amfani da ilimin da suka samu ta hanyar da data dace wajen bunkasa cigaba al’umma da kuma kasa baki daya.
Ya kuma bayyana cewa taron zai cigaba da gudana a rufaffen dakin taron na ‘convocation Arena’ dake jamiar tsawan kwanaki hudu inda za a gabatar da jawabai daban-daban daga malamai da kuma karrama fitattun mutane da suka hadarda tsohon gwamna Kano a zamanin soji kanal Sani Bello mai ritaya da fitaccen dan kasuwar nan Alhaji Auwalu A.A. Rano da digirin girmamawa bisa irin gudunmawa da suka baiwa ilimi da kuma al’ummar da suke fito daga Cikinsu.
Suma a nasu bangaren, daliban da suka kammala digirin na farko a bangarori daban daban sun nuna farin cikinsu bisa irin gudunmawa da jami’ar ta basu domin ganin sun cimma burinsu na rayuwa.
Taron ya samu halartar alumma da dama daga ciki da wajan kasarnan.