DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO
Sabon shugaban hukumar zakka da Hubusi ta jihar Kano Barrista Habibu Muhammad Dan Almajir ya bukaci alumma dasu baiwa hukumar hadin kan da ya dace domin gudanar da ayyukanta kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Barrista Dan Almajir ya bayyana hakane a yayin da aka yi masa rakiya domin kama aiki a matsayin sabon shugaban hukumar na jihar Kano.
Sheikh Dan àlmajiri ya ce hukumar zakka an samar da ita ne domin karbar zakka daga hannun mawadata da suke cikin al’umma da kuma rabata ga mabukata wanda hakan yake tallafawa mutuka wajen rage Talauci da fatara da kuma sanya kauna a tsakanin alumma.
KU KARANTA: Darikar Tijjaniyya Ta Yabawa Gwamnan Kano Bisa Nadin Barista Dan-almajiri Shugaban Hukumar Zaka
Ya ce babban aikin hukumar zakka da hubusi shine tallafawa raunana dake cikin alumma ta bangarori daban-daban, amma hakan bazai samu ba sai an samu cikakken goyan bayan gwamnati da kuma mawadata.
Ya ce hakika shugabancin hukumar a yanayin da ake ciki yana da mutukar hadari musamman na irin wadannan hukumomi da suka shafi rayuwar alumma kai tsaye duba da yanayi na matsin tattalin arziki da ake ciki.
Ya ce lamarin zakka yana da kalubale daban daban domin ita zakka cewa akayi a karbo
daga hannun mawadata daga abunda Allah ya basu sannan kuma a raba ga mabukata, a dan haka dole sai mawadatan sun bada cikakken hadin kai aikin zai gudana kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
A karshe ya yabawa gwamna jihar Kano Abba kabir Yusuf da mataimakinsa kwamared Aminu Abdussalam bisa kyakyawan zaton da sukayi masa wajen bashi wannan aikin, ya kuma bukaci alumma dasu taya su da addua domin ganin sun sauke nauyin da aka dora musu.
Taron ya samu halartar alumma da dama da suka hadarda shugaban jamiiar Khalifa Isiyaka Rabi’u KHAIRUN farfesa Abdurrashid Garba da Alhaji Ali Abdurrahman da sauran su.